✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NEMA ta raba kayan abinci ga ’yan gudun hijira 16,000 a Borno

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa (NEMA), ta raba tallafin kayan abinci da na amfanin yau da kullum ga ’yan gudun hijira 16,000 a…

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta Kasa (NEMA), ta raba tallafin kayan abinci da na amfanin yau da kullum ga ’yan gudun hijira 16,000 a jihar Borno.

Da yake jawabi a lokacin kaddamar da rabon kayan agaji da cibiyar jinkai ta Sarki Salman ta bayar a sansanin ’yan gudun hijira na El-Miskin da ke Jere, Darakta Janar na Hukumar NEMA, Ahmed Mustapha Habib ya ce manufar yin hakan ita ce rage wahalhalun da mutanen ku fuskanta, musamman yadda ambaliyar ruwa ta yi musu barna.

Ya kara da cewa, kowanne daga cikin magidanta 16,000 ya samu kilogiram 25 na shinkafa, kilogiram 25 na wake, kilogiram 25 na gari da masara da taliya da tumatur da man girki da kayan yaji da barguna da dai sauransu.

A cewarsa, NEMA za ta ci gaba da bai wa gwamnatin jihar Borno goyon baya wajen sake tsugunar da ’yan gudun hijirar zuwa garuruwan kakanninsu, yayin da sojojin Najeriya ke ci gaba da samun galaba a yakin da suke yi da ’yan ta’addan Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas.

“Sannu a hankali al’amura na komawa daidai a yankin Arewa maso Gabas, tare da jajircewar Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum.

“Muna ganin wani aikin alheri daga Gidauniyar KSRelief, cibiyar ta sake ba da gudummawar kayan abinci ga mutane 16,000 don ciyar da su a Jihar ta Borno a  zagaye na biyu”.

Da yake jawabi Gwamna Babagana Umara Zulum ya yaba wa hukumar ta NEMA tare da nuna jin dadinsa ga Shugaban Hukumar NEMA da taimakon jinkai na Sarki Salman da kuma Gidauniyar Dangote da aka kawo a jihar ta Borno.

“Wannan ba shi ne karon farko da gidauniyar agajin jinkai ta Sarki Salman ke kai kayan agaji ga jihar Borno ba, tun a shekarar 2018 aka fara samar da kayan agaji, kuma har ya zuwa yanzu muna addu’ar Allah ya sakawa Masarautar Saudiyya da alkhaitimsa.”

Shi ma da yake nasa jawabin, wakilin gidauniyar Sarki Salman ta bayar da agajin gaggawa a Najeriya, Al-yuosuf Abdulkarim ya ce, “Wannan tallafin ya zo ne a matsayin karin tallafin da gwamnatin kasar Saudiyya ta bayar  zuwa kasashen da abin ya shafa a duk fadin duniya.”