✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NECO ta kara wa’adin rajistar jarabawar 2022

Za a fara jarabawar daga ranar 27 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Agusta,

Hukumar shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta tsawaita wa’adin rajistar jarabawar kammala makatantun sakandare zuwa 12 na daren 20 ga watan Yunin 2022.

Shugaban Sashen Yada Labaran hukumar, Azeez Sani ne ga bayyana hakan, in da ya ce a baya hukumar ta ware ranar 30 ga watan Mayu a matsayin ranar rufewa.

Haka zalika Sani ya ce an shirya fara jarabawar daga ranar 27 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Agusta, kuma darussa 76 za a yi jarabawar kansu.

Haka kuma ya ce babu wani wa’adi da a yanzu hukumar za ta kara, tare da yin kira ga ma’aikatun ilimi da shugabnnin makarantun sakandare, da sauran masu ruwa da tsaki da su yi amfani da wannan dage jarabawar ta hanyar da ta dace.