✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NECO ta fitar da sakamakon jarabawar kammala firamare

Hukumar jarabawa ta kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar 2020/2021 shiga makarantun Sakanadare Gwamnatin Taraya 110 a duk fadin kasar. Mukaddashin Rajistaran NECO, Godwill…

Hukumar jarabawa ta kasa (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar 2020/2021 shiga makarantun Sakanadare Gwamnatin Taraya 110 a duk fadin kasar.

Mukaddashin Rajistaran NECO, Godwill Obioma, ya ce dalibin da ya fi kwazo a jarabawar dan Jihar Anambra ne wanda ya sami kashi 199 cikin 200, na biyu kuma dan jihar Imo ne da kashi 198 sai n auu da 3rd daga Ogun tare da 197.

Da ake gabatar da sakamakon a Abuja ga Ministan Ilimi, Adamu Adamu, Obioma ya ce jarrabawar ta gudana ba tare da wata matsala ba kuma masu sa ido na waje da na ciki sun sanya ido tare da kulawa.

Dalibai 92,591 ne suka yi rajistar jarbawar ta ranar 17 ga Oktoba, 70,580 suka rubuta wasu 16,714 ba su samu rubutawa ba saboda wasu dalilai.