Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta gano wata kontaina dauke da kwayoyin Tiramol kimanin miliyan biyar a Tashar Ruwan Onne, Jihar Ribas.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce an kama miyagun kwayoyin da aka boye a cikin katan-katan 1,387 ranar Talata, bayan wani binciken hadin gwiwar jami’an hukumar da na Kwastam kan wata kontaina wacce tuni hukumar ke sa ido a kanta.
- Yadda Kwastan ta kama tankar mai makare da shinkafar waje a Katsina
- Gwamnatin Tarayya ta shiga rikicin ’yan kwadago da El-Rufai
Ya kara da cewa Hukumar ta kame wani mutum mai shekara 42 a yankin Jimeta na Jihar Adamawa dauke da buhu 13 na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 166.
Hukumar ta kuma cafke wani mai shekara 35 dauke da hodar Ibilis mai nauyin kilogiram 16.1 a yankin Ngurore a Jihar ta Adamawa.
Shugaban hukumar NDLEA, Mohamed Buba Marwa, ya jinjina wa aikin hadin gwiwar hukumar da sauran hukumomin tsaro da suka kai ga samun nasarori.