✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama matar da ta ɓoye hodar iblis a al’aurarta

An buƙaci ta haɗiye ƙwayoyin hobar iblis 70, sai dai bayan haɗiye 67 ta ƙasa haɗiye sauran.

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya, NDLEA ta sanar da cafke wata mata da ta ɓoye hodar iblis tana shirin tafiya ƙasar Iran.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar, ya ce an kama matar ce a filin jirgin sama a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.

Babafemi ya ce matar ta ɓoye hodar iblis ɗin a cikin al’aurarta da cikinta da kuma a wata jaka.

A cewarsa, matar mai suna Ihensekhien Miracle Obehi, wadda ta saka hijabi domin ƙoƙarin tsallake binciken jami’an tsaro, an cafke ta ne a Lahadin da ta gabata lokacin da take yunƙurin shiga jirgin Qatar Airline zuwa Doha, kafin ta wuce Iran.

Ya ƙara da cewa yayin bincike, an gano matar ta saka ƙunshin hodar iblis har uku cikin al’aurarta, sannan ta saka wani a jakarta sai kuma ta haɗiye ƙwayoyi 67 a cikinta.

Sai dai mai magana da yawun hukumar ya ce an tilasta wa matar yin aman ƙwayoyin da kuma ƙunshin waɗanda ta haɗiye a cikinta da na ɓoye a al’aurarta.

Obehi ta yi iƙirarin cewa an buƙaci ta haɗiye ƙwayoyin hobar iblis 70, sai dai bayan haɗiye 67 ta kasa haɗiye sauran — inda ta yanke shawarar saka su a al’aurarta, a cewar Babafemi.