✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama makaho da kuturu dauke da Tabar Wiwi

An kama su ne Jihohin Kano da Osun

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) sun kama wani makaho da kuturu dauke da Tabar Wiwi a Jihohin Kano da Osun.

Mutanen da aka kama su ne Aliyu Adebiyi, wani makaho mai kimanin shekara 67 wanda aka samu kilogiram 234 a gidansa, da kuma wani Owena Ijesa da ke Karamar Hukumar Atakumosa ta Jihar Osun.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Lahadi a Abuja.

Ya ce dilan kwayar ya ajiye ta ne a gidansa a kan kudi Naira 6,000 da aka biya shi na wata uku.

Kazalika, ya ce an kama wani kuturu mai suna Haruna Abdullahi mai shekara 45 a garin Garko da ke Jihar Kano ranar Alhamis, 19 ga watan Janairun 2023 da kilogiram 2.2 na Tabar Wiwi da kwayoyin diazepam da Exol.

Babafemi ya kuma ce hukumar ta kama wasu masu safarar kwayoyi da ke kokarin shigo da Hodar Iblis din da aka kulle a wani kunshin ganyen shayi da aka shigo da shi daga kasashen Brazil da Kanada a filin jirgin sama na Akanu Ibiam da ke Enugu da tashar jiragen ruwa ta Tin Can da ke Legas.