✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NDLEA ta kama hodar ibilis ta Naira biliyan 194 a Legas

NDLEA ta ce wadanda aka kama bisa zargin badakalar hodar, tun a 2018 take neman su ruwa a jallo

Jami’an Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta bankado wata ma’ajiyar hodar ibilis a yankin Ikorodu, Jihar Legas, mai dauke da hodar ta iblis da yawanta ya kai tan 1.8, kwatankwacin kilogram 1,855.

Bayanan jami’an sun nuna hodar ibilis din da aka kama darajarta ta kai Dala miliyan 278,250,000, kwatankwacin biliyan N194.775.

An kuma cafke wasu mutum hudu, ciki har da manajan rumbun ajiyar da wani dan asalin kasar Jamaica da ake zargi da hannu a harkar hodar ibilis din.

NDLEA ta ce duka wadanda aka kaman gaggan masu safarar miyagun kwayoyi ne wadanda hukumar ke nema tun 2018.

Da yake karin haske kan lamarin, Daraktan Yada Labarai na NDLEA, Femi Babafemi, ya shida wa kafar yada labarai ta PM News cewa rumbun ajiyar da aka gano hodar na wani gida ne a rukunin gidajen Solebo, Ikorodu.

Ya kara da cewa, a ranar Lahadin da ta gabata suka kai samame ma’ajiyar inda daga bisani suka samu nasarar damko wadanda ake zargin.