✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta ƙone gonar tabar wiwi a Edo

An kama wasu bisa zargin mallakar wiwi mai nauyin kilo 125.3; da kwalaben maganin Kodin 30 a Kano.

Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta lalata sama da tan uku na tabar wiwi a wani dajin Jihar Edo.

Sanarwar da Daraktan Labarai na Hukumar NDLEA, Mista Femi Babafemi, ya fitar ta ce an gano tabar ce a kadada 1.577683 na gonaki.

Babafemi ya ce jami’ansu sun kai farmaki a dajin Oloma-Okpe da ke Karamar Hukumar Akoko Edo tare da lalata kilo 3,944.2 na tabar wiwi a gonakin.

Haka jami’an NDLEA a Edo a ranar Alhamis, 14 ga Maris, sun kama wani mai suna Kole Samuel mai shekara 50, dauke da kilo 75 na abubuwan da ke kashe mutane, an kuma kama shi ne a kasuwar Otuo ta Karamar Hukumar Owan ta Gabas.

Haka an kama kilo 2 na tabar wiwi a wajen direban wani kamfanin sufuri, Ikechukwu Obliged, a mahadar Shagamu, a Jihar Ogun, a ranar Laraba 13 ga Maris.

Kuma ya ce an kama wasu mutum biyu Ali Amadu mai shekara 27 da Adamu Hassan mai shekara 33 bisa zargin mallakar wiwi mai nauyin kilo 125.3; kwayoyin taramadol 3,400; da kwalaben maganin Kodin 30 a Jihar Kano.

“An kama su ne a ranar Litinin, 11 ga Maris, a Gadar Tamburawa, da Juma’a 15 ga Maris, a Tsamiya Babba, Hotoro.

“Kuma an kwato kilo118 na wiwi a wani rumbun ajiya a yankin Masaka a Jihar Nasarawa a ranar Asabar, 16 ga Maris,” in ji shi.

Babafemi ya ruwaito Shugaban Hukumar NDLEA, Brigediya Janar Buba Marwa (mai ritaya), yana yaba wa jami’an hukumar kan yadda suka kara kaimi wajen gudanar da aikinsu.