Shugaban Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) Bigediya Janar Buba Marwa (mai ritaya) ya bukaci a fara yi wa matasa masu yi wa kasa hidima gwajin miyagun kwayoyi.
A cewarsa, kamata ya yi a sanya gwajin ya zama tilas kafin kowane matashi ya shiga sansanin bayar da horo na Hukumar Kula da Matasa Masu yi wa Kasa Hidima (NYSC).
- 2023: Kwankwaso ya zama dan takarar Shugaban Kasa na NNPP
- Babu wanda na kullata a cikin wadanda suka yi takara da ni – Tinubu
Shugaban ya ce hakan na cikin burin da suke da shi na rage yawan ta’ammali da miyagun kwayoyi musamman a tsakanin matasa.
Buba Marwa ya bayyana hakan ne lokacin da ya tawagar Shugaban NYSC, Mohammed Fadah, ta ziyarce shi a hedkwatar hukumar da ke Abuja ranar Laraba.
A cewar Buba Marwa, “Akwai bukatar a fara yi wa matasanmu gwajin kafin su shiga sansanonin ba da horo na NYSC. Da zarar suka tabbatar za a yi musu gwajin a sansanonin, to tabbas za su kiyaye ta’ammali da kwayoyin.
“Babbar manufar ita ce domin a gano masu amfani da kwayoyin tun da wuri, kuma hakan na da nasaba da shirinmu na yakin da muke yi da kwayoyin da muka yi wa lakabi da WADA.
“Wannan matsalar ta tasamma yi wa Najeriya katutu, mun kuduri aniyar ganin mun kawo karshenta, amma ba za mu iya yi mu kadai ba, muna bukatar hukumomi irin NYSC,” inji Buba Marwa.
Tun da farko a nasa jawabin, Birgediya Janar Fadah, ya ce sun kai ziyarar ce don yaba wa NDLEA kan irin taimakon da take ba su, tare da neman karin hadin gwiwa a daidai lokacin da take kokarin sake bude sansanoninta a fadin Najeriya.