✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA na neman DCP Abba Kyari ruwa a jallo

Ana zargin DCP Abba Kyari da hada-hadar miyagun kwayoyi.

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta ayyana Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda da aka dakatar, DCP Abba Kyari a matsayin wanda take nema ruwa a jallo bisa zargin harkalla ta miyagun kwayoyi.

Kakakin Hukumar NDLEA, Mista Femi Babafemi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da ya gudana ranar Litinin a Abuja.

Majiyar mai tushe daga Hukumar NDLEA ta ce bincike ya nuna cewa DCP Kyari daya daga cikin ’ya’yan wata babbar kungiya ta kasa-da-kasa da ke hada-hadar miyagun kwayoyi a fadin duniya.

A watan Yulin bara ne Rundunar ’yan sandan Najeriya ta dakatar da Abba Kyari daga aikin dan sanda sakamakon zargin karbar na goro da Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI ke yi masa.

Hukumar Kula da Harkokin ’Yan Sanda ta dauki matakin dakatar da DCP Kyari ne biyo bayan shawarar da Sufeto Janar na ’Yan Sanda Usman Alkali Baba ya bayar.

A halin yanzu dai ana ci gaba da bincike kan zargin Abba Kyari da karbar cin hanci a hannun matashin dan Najeriya kuma mazaunin Amurka mai suna Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushpuppy, domin kamawa da kuma muzguna wa wani abokin harkarsa, Kelly Vicente.

Hushpuppy ya bayyana cewa ya bai wa Mista Kyari rashawar ce yayin da Hukumar Tsaron FBI ta Amurka ta kama shi bisa zargin aikata damfara da zamba a kan kamfanoni da daidaikun mutane a fadin duniya.