✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDE za ta koya wa matasa dubu 1 sana’o’i a Kaduna

Hukumar Koyar da Sana’oi ta Kasa (NDE) ta shirya tsaf domin koya wa matasa da mata marasa aikin yi dubu 1 sana’o’i domin dogaro da…

Hukumar Koyar da Sana’oi ta Kasa (NDE) ta shirya tsaf domin koya wa matasa da mata marasa aikin yi dubu 1 sana’o’i domin dogaro da kai a Jihar Kaduna.

Matasan maza da mata za a koya masu yadda ake yin sabulu da dinki da gyaran wayar hannu da gyaran gashi da kuma gyaran kwanfuta.

Kodinetan Hukumar NDE a Jihar Kaduna Sani Maiwada ya shaddawa Aminiya cewa duk wadanda suka samu halartar horon za a ba su takardar shaida tare da tallafi.

Ya ce za a koya masu wadannan sana’oi ne har na tsawan watanni uku sannan kuma wadanda za su koyi yadda ake hada sabulu da man gashi na mata su makonni biyu kacal za su yi.

Ya ce mata 400 za a koya masu yadda ake hada man gyaran gashi da na  mata da kuma sabulai.

Wasu 400 kuma za a koya masu gyaran wayar hannu da dinki da gyaran kwanfuta . Sannan  wasu 150  za a koyar da su sana’oi biyu a cibiyoyin koyar da sana’oi da ke Zariya da Kaduna da Kafanchan. Mutum hamsim (50) kenan a kowace cibiya sai kuma ragowar mutum  hamsin (50) za a bi su har inda suke ne a koya musu sana’o’in wato School on Wheels.

Kodinetan ya ce tsarin bi har inda mutane suke wajen koya musu sana’o’in ya kunsyhi bangarori uku ne wato na kafinta da gyaran lanrtarki da kuma gyaran gashi.

Ya shawarci wadanda za su koyi sana’o’in da su mayar da hankali don su ci gajiyar shirin.