Hukumar Samar da Aikin yi NDE ta fara koyar da sana’o’in hannu ga ‘yan gudun hijira dubu ashirin da biyar a Jihar Adamawa domin samin rufin asirin rayuwa kafin su koma garuruwansu.
Mista Keneth Maigida wadda shi ne shugaba mai kula da harkokin koyan sana’o’in hannun ne ya bayyana hakan a sansanan ‘yan gudun hijira da ke Malkohi, inda ya ce za a koyar da sana’o’i daban-daban har goma sha daya ga ‘yan gudun hijiran da ke sansanin gudun hijira da kuma wadanda ke cikin gari.
Keneth ya ce hukumar ta samarwa wadansu ayyukan yi sannan a halin yanzu tana koyar da matasa dubu biyu sana’o’in hannu a duk kananan Hukumai ashirin da daya domin rage yawan masu zaman banza a gari.
Maigida ya ce bayan an gama koyar da matasan sana’o’in hannun, za a basu bashin kudi wanda zai taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu “Mun yanke shawarar basu bashi wanda zai taimaka musu wajen fara sana’o’in hannun da suka koya, wanda kuma za su biya a hankali ba tare da riba ba”. Inji shi.
Sannan ya yi kira ga matasan da su yi amfani da wannan damar domin samar wa kansu abin yi wanda zai taimakawa rayuwarsu idan suka dage su yi suka yi.
Shugaban Majlisar Jihar Adamawa, Alhaji Kabiru Mijinyawa a na shi bangaren, ya ce Gwamnatin Jihar za ta yi iya kokarinta wajen basu goyon baya domin gudanar da wadannan ayyukan.
“Dalilin wanna koyon sana’o’in hannun shi ne a samar wa matasa da basu da aikin yi abin yi domin taimakawa kansu,” Inji shi.
Sana’o’in da za a koyar da su sun hada da kiwon kaji da koyar da noman rani da koyan girke-girke da dinki da hada takalma da dai sauransu.