Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa (NCDC) ta kora daliban da suka koma karatu bayan gwamnatin jiha ta bude makarantu a jihar Kuros Riba.
‘Yan makaranta sun yi cirko-cirko a waje bayan jami’an NCDC sun kai samame a makarantar West African People’s Institute (WAPI) da ke garin Kalaba, inda suka rufe ta tun da misalin 8.00 na safiyar Talata.
A karshen makon jiya ne Gwamna Ben Ayade ya ba da umarnin bude makarantu uku a mazabun ‘yan majalisar tarayya uku a jihar a matsayin gwaji.
Sauran makarantun biyu su ne Sakandaren Gwamnati da ke Egoli a karamar Hukumar Ogoja da takwararta da ke garin Ikon a mazaba ta tsakiya.
Jihar Kuros Riba ita ce kadai jihar da ba samu bullar cutar coronavirus ba a fadin Najeriya, inda hukumar NCDC ke kan gaba wajen kokarin dakile yaduwarta.
Bullar cutar coronavirus ta yi sanadiyyar rufe makarantu da sauran wuraren taruwan jama’a wanda yanzu aka fara sassautawa.