Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce ta umarci dukkan kamfanonin layukan sadarwar da su kammala tantancewa da kuma hada layukan katin SIM da lambar ɗan ƙasa (NIN) kafin ranar 14 ga Satumba, 2024.
NNC ta bayyana hakan ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun, Daraktan hulɗa da jama’a na NCC, Mista Reuben Muoka a ranar Laraba.
- Soja ruwa ya kashe wani ya sace motarsa a Abuja
- An ɗaure ‘yan Najeriya kan takardun auren bogi 2,000 a Birtaniya
Sanarwar ta ce, umarnin na da nufin tabbatar da cikakken bin ƙa’idojin haɗe lambar NIN da katin SIM.
A cewar sanarwar, ya zuwa yanzu, sama da layukan SIM miliyan 153 aka samu nasarar hada su da lambobin NIN, wanda ke nuna kyakkyawan tsarin aiki na kashi 96 cikin 100, daga kashi 69.7 cikin 100 a cikin Janairun 2024.
“Yayin da muke gab da matakin ƙarshe na wannan muhimmin tsari, NCC na neman karin haɗin kan al’ummar Najeriya domin cimma daidaito na 100 bisa 100.
“Cikakken hada katunan SIM zuwa lambobin NINs yana da mahimmanci don inganta amana da tsaro ta fasahar sadarwar tattalin arziki.
“Hakan zai yana rage haɗarin zamba da aikata laifuka ta yanar gizo, kuma yana tallafawa wajen yin hulɗar kasuwanci ta yanar gizo, mu’amala da banki ta fasahar zamani da yin harkokin hulɗa da kuɗi ta wayar hannuda kawo cigaban tattalin arziki,” in ji shi.
Ya ce akwai ƙararraki, inda mutane suka mallaki katinan layukan sadarwa SIM da ba a saba gani ba, wasu sun wuce 100,000.
Hukumar ta NCC ta ce ta kuma jajirce wajen haɗa kai da hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki wajen daƙile sayar da katin SIM da aka riga aka yi rajista.