✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NCC ta ci tarar MTN naira tiriliyan daya

A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar da ke Kula da Kamfanonin Sadarwa wato NCC ta ci tarar kamfanin MTN fiye da naira Tiriliyan…

A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar da ke Kula da Kamfanonin Sadarwa wato NCC ta ci tarar kamfanin MTN fiye da naira Tiriliyan daya domin gazawarsa wajen rufe layukan masu hulda da shi, wadanda ba su yi rijista ba har wa’adin yin hakan ya wuce.

Wata sanarwa da MTN ya fitar ta tabbatar da cewa an ci tararsa, sai dai kamfanin ya ce yana ci gaba da tattaunawa da Hukumar NCC a kan rufe layukan wayoyin mutanen da ba su yi rijista ba. Hukumar ta ce ta ci tarar kamfanin ne naira dubu dari biyu a kan kowane layi miliyan biyar da dubu dari daya wadanda ba a yi musu rijista ba.
Wannan shi ne karon farko da aka ci tarar wani kamfanin sadarwa makudan kudi saboda rashin bin umarnin hukumar.
Masu amfani da layukan kamfanin MTN dai sun sha yin korafi wajen rashin biyan bukatarsu.
Hakazalika, darajar hannun jarin kamfanin wadda na kasar Afirka ta Kudu ya fadi da fiye da kasha 12 cikin 100, sakamakon rahotannin da ke cewar za a ci tarar kamfanin.
An dai fara rijistar layukan wayar ne a shekarar 2012 kuma a watan Agustan da ya wuce ne hukumar ta fahimci cewa fiye da layuka 38 ba a yi musu rijista ba yadda yakamata. Daga nan hukumar ta bayar da wa’adin wata guda don yin hakan, ko kuma su fuskanci tara.

Ra’ayin jama’a kan tarar

Jibrin Jibo: A ra’ayina su kamfanin wayar salula na MTN sun yi kuskure da suka ki bin doka da oda saboda bai kamata su yi watsi da dokar da hukumar NCC ta kafa ba amma ni ina ganin ya kamata a yafe musu don su ma su sami sauki, don gaskiya kudin ya yi yawa. Ya kamata hukumar NCC ta sassauta musu.
Alhaji Auwalu Azare: Ni a ra’ayina ina goyon bayan tarar saboda kin toshe layukan mutanen da ba su yi rajista ba. Dalili shi ne yin rajistar wata hanya ce ta tsaro, duk kasashen da suka ci gaba babu wacce za ka je ka sayi layi ba tare ka yi masa rajista ba, idan kai bako ne akwai adadin kwanakin da za ka yi. Don daga rajistar ake sanin bayananka, daga wace kasa ka zo, me ye sana’arka, kuma me ya kawo ka, amma mu a nan Najeriya saboda sun rainamu sai su rika taka doka yadda suka ga dama.
Rabi’u Yunus: Gaskiya da na ji wannan labarin na ji dadi sosai domin a halin da muke cikin kowa ya yi ba daidai ba, to ya kamata a nuna masa kuskurensa, idan ya taka doka dole a nuna masa ya yi kuskure. Dama mu kodayaushe muna so a rika samun ci gaba. Ka ga matakin da hukumar NCC ta dauka zai zama darasi ga sauran kamfanonin waya da ke kasar nan.