Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya, ta bai wa kamfanin jiragen sama na Azman damar ci gaba da gudanar da harkokinsa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kamfanin na Azman ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.
Sanarwar da kamfanin ya fitar ta ce bayan gamsuwa da Hukumar NCAA ta yi da shi dangane da kiyaye dokokinta da sharundan da ta gindaya na samar da kwanciyar hankali ga abokanan huldarsa, a yanzu an janye dakatar wa da aka yi masa.
Ana iya tuna cewa, a ranar 15 ga watan Maris ne NCAA ta dakatar da kamfanin daga zirga-zirga a fadin kasar.
NCAA ta ce matakin hakan ya yi daidai da tsarin dokokin da ta gindaya a kundin da ta kirkira a 2006.