✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nazarin kalaman azanci domin kyautata rayuwa 11

Assalamu alaikum. Yau ma ga shi za mu dora kan darasin da muka faro baya:Ga wani muhimmin kalami da wani magabaci da ban tantance sunansa…

Assalamu alaikum. Yau ma ga shi za mu dora kan darasin da muka faro baya:
Ga wani muhimmin kalami da wani magabaci da ban tantance sunansa ba ya fada, inda yake cewa: “Kada ka bari sai gobe, abin da za ka iya yi a yau.”
Wannan batu yana da tsananin muhimmanci da tasiri a rayuwarmu, musamman idan muka nazarce shi da idon basira. Kamar yadda za mu gani, abu na farko da za mu iya tsinkaya daga batun nan shi ne, muhimmancin lokaci a rayuwa. Za mu iya gane haka idan muka dan yi nazari kan muhimman tubalan lokaci guda uku, watau jiya da yau da kuma gobe. Cikin wadannan tubala ne za mu iya fahimtar wannan muhimmin batu.
Idan muka nazarci jiya, za mu fahimta da cewa ta riga ta wuce, kuma ba za ta dawo ba har abada. Duk abin da mutum ya aikata a cikinta, ya riga ya shude, idan na kirki ne, mutum ya ci riba ke nan. Idan kuma ba na kirki ba ne, to ya ci baya ke nan. Idan ma mutum bai aikata komai ba a cikin jiya din nan, wannan ya nuna cewa mutum ya yi asarar jiya din nan ke nan, domin kamar yadda muka ambata, ta wuce, ba za ta yo ribas ta dawo ba domin ka aikata abin da kake son aikatawa. Amma duk da haka, muhimmancin jiya din nan shi ne, mutum zai samu damar nazarinta, sannan ya gano abin da ya aikata a cikinta. Idan wani abin kokari ya yi, zai yi farin ciki, sannan ya kara kokari a yau domin ganin cewa ya ninka aikata irinsa a yau. Idan kuma ba mai kirki ba ne, sai mutum ya yi nadama a yau, sannan ya kuduri aniyar hana kansa aikata irinsa a yau. Haka dai batun yake idan mutum ya zama bai aikata komai ba a jiya, sai ya himmatu domin ganin ya aikata wani abu mai muhimmanci a yau da Allah Ya nuna masa.
Ita kuwa yau, wacce ita muke ciki, tsananin muhimmancinta yana da yawa, musamman ma ganin cewa wata dama ce da muka sake samu, wacce ta bambanta da jiya. Tsagwaron darasin wannan kalami namu na sama, yana kunshe ne a cikin ita yau din. Don haka sai mutum ya yunkura, ya aikata abin kirki a cikin yau din. Zai yi haka ne ta kwatanta abubuwan da ya yi a jiya, domin sake kwatanta su ko kuma ma ya ninka su, musamman idan masu muhimmanci ne. Yau za ta ba mutum damar kauce wa fadawa cikin irin kuskuren da ya aikata a jiya, sannan idan ma ya zama bai aikata komai ba a jiyan, sai ya yunkura, cikin himma domin ganin cewa ya aikata wani abu na amfani a rayuwarsa.
A nan, ya kamata mu sake nazarin batun nan dai namu na sama, cewa duk abin da ka san za ka iya aikatawa a yau, ko a yanzu, to ka aikata shi kawai gaba gadi, kada ka ce bari in bari sai anjima ko kuma sai gobe. Wannan hukunci da ka yanke yana da hadari sosai, domin kuwa a yau ne kuma a yanzu ne kake da iko da damar yin wani abu, domin ba ka san yadda za ta kasance anjima din ko goben ba. Idan kuwa ka aikata wani abu yanzu-yanzu, to ka karu ke nan, kuma ka rage wa kanka wata wahala, wacce idan ka bari cewa sai gobe ko sai anjima, idan har Allah Ya kai mu anjima din ko goben, to tana iya zuwa da irin nata matsalolin da bukatun, wadanda suka sha bamban da na dazu ko na jiya din. Ke nan, ka samu aiki biyu ko uku ke a lokaci guda, maimakon daya, domin na dazu ko na jiya na nan ba ka aikata ba, sannan ga kuma wani na yanzu da ya kawo kansa, wanda kuma ya zama dole sai ka aikata shi. Domin kauce wa haka, sai ka mike kawai, yanzu-yanzu, ba sai anjima ba, ka aikata abin da za ka iya aikatawa.
Idan muka duba tubali na uku kuma, watau gobe, za mu fahimta da cewa ba ta zo ba tukunna, kuma ba mu da tabbacin zuwanta, amma duk da haka ba shantake kafa za mu yi mu sanya idon zuwan nata ba kawai. A’a, za mu yi wani dan kokari ne irin daidai namu, domin kuwa a matsayinmu na mutane, muna da bukatu da burace-burace da muke da nufin aikatawa idan mun samu dama. Ga shi kuma mun aikata wani abu jiya, ba mu gama ba, muka ci gaba da shi yau, ba mu kammala ba, sai mu jefa shi cewa, idan Allah Ya nuna mana gobe lafiya, za mu ci gaba. Wannan buri na cewa gobe, in Allah Ya kai mu zan ci gaba da kaza, shi ne abin bukata, shi ne tsarin da za ka sanya a zuciyarka, kuma kada ka sake ya kauce daga kwakwalwarka; idan da hali ma, dauki alkalami ka rubuta shi, domin kada ka mance.
Da zarar Allah Ya nuna maka gobe din nan, ka ga kana da burinka, kuma ka yi nazarin hanyoyin da za ka bi domin cin ma aiwatar da shi. Idan Allah Ya ba ka iko da damar aiwatarwa, ka ci gajiya da ribar wannan lokaci ke nan. Har kullum ita rayuwarmu, ba tabbas ke gare ta ba, don haka a matsayinka na mutum, sai ka yi iyaka kokarinka daidai ikonka. Babban abin da dai ba a so shi ne zaman dirshan, watau zaman kashe wando. Wannan babbar cuta ce, babbar illa ce da ke dakushe ci gaban mutum da al’umma baki daya.
Idan muka duba darasinmu na yau, za mu fahimta da babbar fa’idar lokaci, sannan kuma mu gane cewa kasala halayya ce marar amfani ga dan Adam. Wadannan abubuwa biyu, su za mu tantance domin fa’idantar da rayuwarmu ta yau da kullum. Shi dai lokaci, mu yi amfani da shi a yau, a yanzu, ba sai anjima ko sai gobe ba. Ita kuwa ganda da kasala da kyuya, duk mu kauce musu, mu yake su, domin abokan gaba ne, wadanda ke hana mana ci gaba a rayuwa.