✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nazarin kalaman azanci domin kyautata rayuwa (06)

Jama’a masu karatu, Assalamu alaikum. Yau ma dai kamar yadda muka faro makonni biyar da suka gabata, za mu ci gaba ne da fashin bakin…

Jama’a masu karatu, Assalamu alaikum. Yau ma dai kamar yadda muka faro makonni biyar da suka gabata, za mu ci gaba ne da fashin bakin wasu kalaman azanci domin kyautata rayuwa da muka ci karo da su a wurare daban-daban. Kamar yadda bayani ya gabata, irin wadannan kalamai na hikima, magabata ne masu fasaha da hikima da basira suka furta su, mu kuma za mu ci gaba da amfana da su, kasancewar hikima kayan al’umma ce. Allah Ya albarkace mu da dacewa da tasirin kowace hikima, amin.
Yanzu kuma sai mu shiga batu na gaba da muka zakulo muku, watau inda wani mai hikima shi ma ya ce: “Ingancin rayuwar mutum daidai yake da dagewarsa a kan kyawawan sakamako, koma mece ce sana’arsa ko aikinsa.”
Babbar magana, wai dan sanda ya ga gawar soja! Kamar yadda rayuwa take, kowane mutum yana son ya ga cewa ya samu ci gaba, ya samu gamsassar nasara a rayuwarsa. Idan aikin gwamnati ko na kamfani mutum yake yi a rayuwarsa, yana matukar bukatar ya ga cewa ya samu nasara, ya samu ci gaba ta fuskar karin girma da sauransu. Idan kuma wata sana’a yake yi ta kashin kansa, babu shakka yana son ya ga cewa ya samu nasarar ci gaba, yana son ya ga sana’ar tasa ta habaka, ya samu riba mai yawa, ta yadda zai fadada sana’ar tasa. To, abin tambaya a nan shi ne, ta yaya mutum zai samu nasara da ci gaba a aikinsa ko sana’arsa da yake yi? Duk da cewa akwai abubuwa da yawa da mutum zai yi domin samun irin wannan gamsassar nasara da ci gaba, amma babban ginshikin da mutum zai sanya gaba shi ne dagewa da jajircewa.
Dagewa ko nacewa da maida hankali kacokan ga aikin da mutum ke yi ko sana’a, su ne za su zama linzaman da za su jagorance shi zuwa ga nasara. Duk abin da mutum zai yi, yana bukatar maida hankali da nacewa da dagewa da jajircewa. Dole ne mutum ya maida hankali, duk abin da mutum zai yi ya nuna cewa da gaske yake yi, ba tare da wasa ko kasala da kasawa ko kosawa ba. Wannan jajircewa ita ce ke gadar ko samar da sakamako mai kyau da cin nasara ga abin da aka tunkari aikatawa. Misali, ko noma kake yi a gona, muddin ba ka dage ka maida hankali da nacewa ba, cikin lokaci gonar taka za ta zama saura, ciyawa ta kucce maka. Idan haka ta faru kuwa, amfaninka ba zai yi nagarta ba, wanda haka zai sanya ka yi asarar noman, maimakon ka samu nasara. Amma idan kullum kana yin abin da ya dace, kuma a lokacin da ya dace, babu shakka za ka ci gajiyar karin maganar nan da ke cewa, bawan damina, tajirin rani.
Idan ka kasance malamin makaranta, madamar kana son samun nasara a aikinka, sai ka dage sosai ka yi aiki wurjanjan. Misali, dole ne ka dage wajen kara karatu, musamman kuma kuma ka kasance mai yawan karance-karance da nazari domin samun sabbin hikimomi da dabarun koyarwa. Ta haka ne za ka iya koyar da dalibai ilimin da ya dace, cikin hikima da dubara, yadda za su fahimta sosai.
A bangare daya, idan kai dalibin ilimi ne, walau a makarantar boko ko kuma ta addini; duka dai sai ka jajirce ka bauta wa makaranta, kafin ka samu abin da kake so. Bautar makaranta a nan ana nufin sai ka dauki matakan koyon ilimin yadda ya dace. Sai ka rika zuwa makaranta a kan lokaci, ka rika mayar da hankali sosai ga abin da malami yake koya maka. Sannan kuma sai ka yi kokarin yin bita da karance-karancen littattafan da suka dace. Ta haka ne za ka karu kuma ka samu ilimi mai yawa kuma mai amfani.
Haka ma duk wata harka da ka sanya kanka a rayuwa, madamar kana son samun nasara a cikinta, ya zama wajibi ka mayar da hankali, ka yi duk abin da ya dace domin ganin ka samu biyan bukata mai gamsarwa, ma’ana ka samu nasara a cikinta. Mayar da hankali na nufin jajircewa, kokarin yin abin da gaske tare da nuna himma ba tare da kasala ba. Allah sa mu dace, amin.