✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Na’urar takaita gudun mota tana taimaka wajen rage hadari – Sanusi Kiri

Wani Jami’in Hukumar Kiyaye Hadurra shiyar  Kaduna Sanusi Ibrahim Kiri, ya ce na’urar takaita gudun mota tana taimakawa kwarai wajen rage hadari a kan hanyoyi.…

Wani Jami’in Hukumar Kiyaye Hadurra shiyar  Kaduna Sanusi Ibrahim Kiri, ya ce na’urar takaita gudun mota tana taimakawa kwarai wajen rage hadari a kan hanyoyi. Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da Aminiya, inda ya yi karin haske game da yadda na’urar take aiki. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya: Za mu so jin karin bayani dangane da sabuwar na’urar takaita gudun mota da hukumarku ke kokarin fito da ita?
Ita wannan na’urar takaita gudun mota wadda ake kira da harshen Inglishi Speed Limit Debice, ana nufin takaita abu ne kada ya yi yawa. Ka san yawancin hadarin da ake samu a kasar nan abubuwa uku ke janyo su, su ne dan Adam da yanayi da ke hade da iska ko ruwa da guguwa da tsawa da sauransu. Sai kuma ita kanta motar.
kididdiga ta nuna cewa kashi 80 cikin 100i na hadarin da ke faruwa a kasar nan dan Adam ke janyo shi. Saboda haka idan muka yi amfani da wannan na’ura wajen rage kashi 80 na hadari mun taimaka. Wannan shi ne manufar kikkiro wannan na’urar.
Misali kamar Speedo Mita wato sikelin da ke nuna gudun abin hawa, ka ga yawancinsu kamar 240 ne idan kana tafiyar 240 mota ba za ta hana ka ba. Amma ita wannan na’ura idan aka ce Kilomita 70 a minti 50 za ka yi amfani da shi da zarar za ka wuce saba’in din na’urar za ta dawo da kai baya.
Mu dama a wannan hukumar kiyaye hadarurruka muna da na’urar Tracking Debice da zarar ka cika gudun mota da ta wuce kima za ta nuna mana wurin da kake kuma zamu kama ka. Yanzu an samu ci gaba ta hanyar wannan na’urar da za ta hana ka, ko na ce za ta takaita ma gudu.
Aminiya:  Zuwa wane lokaci za a fara tilasta aiki da wannan hulan kwano?
Ai yawancin mutanen mu lokacin da aka fara zancen hulan kwano da yawa sun koka da tsadarta, amma yanzu da takai da dawo a 600 ma sai ka samu hulan kwana. Saboda haka ba za mu so mu sake yin kuskure irin na baya ba. Shi ya sa ma ka ce kafin doka ya hau wani direba ko na haya ne ko mai zaman kansa sai mun tabbatar da cewa shi wannan na’ura ta takaita gudu ta wadata sosai.
Muna kuma san mu ga masu gyaranta sun wadatu domin kasan mutane suna iya cewa ai ta lalace shi ya sa ta ki amfani saboda haka idan masu gyararta sun wadatu babu hujja ga direba. Kuma ba mu san kama mutum mu ce ina na’ura ka ce ai babu ita a kasuwa.
Kamar yadda ka sani ne a watan Yuli ya kamata mufara amfani da ita, amma sai aka mayar da shi farkon watan Satumba ka ga an ba ta wajen watanni biyu ke nan. Yanzu haka muna ta tattaunawa da masu ruwa da tsaki a fannin domin samun daidaito.  
Irinsu kungiyoyin masu motoci da kamfanonin masu sayar da motaci da masu sayar da tsoffin kayan mota da sauransu.
Aminiya- kenan ba za’a fara tilasta yin amfani da ita wannan na’ura ba kenan a wannan wata na Satumba?
A kaida daya ga watan taran nan Satumba ya kamata mu fara amfani da dokar amma kasan komai yana san a ciza a kuma hura.
Aminiya: Zuwa yaushe za a fara tilasta dokar?
Ai shi ne na fada maka cewa a doka ya kamata a ce an fara daya ga watan Satumban nan da muke ciki, amma sai dai maganar doka ta hau kan mutane shi ne nake cewa ba za a yi hakan ba sai mun tabbatar komai ya yi daidai. Ma’ana sai mun wadatar da na’urar tukuna a shaguna sannan mu tabbatar da akwai wadatattun masu gyararta a cikin al’umma.
Kamar dai yadda lokacin da wayar hannu ta fito ka ga ai da farko babu masu gyararta sosai, amma daga baya kusan ko ina akwai masu gyara. Sannan muna son jama’a su sani fito da na’urar nan zai kuma taimaka wajen sama matasan mu aikin yi matuka. Kuma ba za mu takaita abin kawai ba ne a cikin birane. A’a muna san har kananan hukumomi daga nan zuwa kauyuka. Domin ko ina ai ana amfani da mota
Aminiya: Idan aka fara aiki da na’urar sannan wasu direbobi suka ki amfani da shi a motarsu, ya ya ke nan?
Kai kuwa ai doka za ta yi aikinta a kansu. Komai ba da kai ake yi ba.
Aminiya: A karshe wane kira za ka yi ga jama’a musamman direbobi dominsu fahimce cewa ita wannan na’ura na da matukar amfani garesu?
Kamar yadda na fada maka ne tun farko cewa muna sa ran wannan na’ura za ta taimaka wajen rage hadarurruka da kashi 80 cikin 100. Bayan haka muna nuna wa direbobi cewa cikin kashi 100 na hadarruka da ke faruwa a kasar nan kashi 65 gudu a mota na fitan arziki ke janyo su. Amma idan kana tafiya a hankali a mota ko kaka wani abu a gabanka hadarin zai zo a hankali.  Saboda haka yana da mahimmaci domin duk abin da za a ce zai taikama wajen rage gudu a mota ai abu ne mai amfani ga rayuwa.