✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nasiha da jan hankali ga shugabannin jam’iyyar APC

A wannan makon, mun samu tsokaci mai take a sama daga mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Kabir Sakaina Layin ’Yangoro Malumfashi (08095968366). A…

A wannan makon, mun samu tsokaci mai take a sama daga mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Kabir Sakaina Layin ’Yangoro Malumfashi (08095968366). A tsokacin nasa, ya yi nazari ne da tariya kan al’amuran sabani da ke faruwa tsakanin shugabannin jam’iyyar APC a wasu jihohin kasar nan, sannan kuma ya bayar da wasu shawarwari, yadda za a shawo kan al’amuran kuma a dinke barakar. Ga abin da yake cewa:
Ya zama wajibi ga duk wani mai kishi ko ci gaban kasarmu Najeriya tare da magoya bayan jam’iyyar APC ya nuna damuwarsa a kan yadda shugabannin jam’iyyar suka kasa magance rikicin da ke ta hauhawa tsakanin wasu daga cikin jagororin jam’iyyar, musamman na Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau da Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso. Haka abin yake a Jiha Sakkwato, tsakanin Alhaji dalhatu Bafarawa da Gwamna Aliyu Wammako. Jihar Adamawa ma haka take da nata rikice-rikicen, musamman tsakanin Gwamna Murtala Nyako das u Buba Marwa.
Kamar yadda masana masu hangen nesa kuma gogaggu a harkar siyasa suka fassara jam’iyyar APC da jirgin ceton Najeriya, haka abin yake ga al’ummar Najeriya. Sun dauki jam’iyyar a matsayin wadda za ta tsamo su daga kagaggen talauci, fatara, yunwa da masifun da aka jefa su ciki, sama da shekaru 10. Amma tun kafin tafiya ta yi nisa, sai ga shi ana ta samun rikice-rikicen da za su iya kawo mummunan nakasu ga samun nasarar jam’iyyar.
Idan muka kalli wata tawagar ’yan jam’iyyar APC, wadda ta hada da tsohon dan takarar shugaban kasa, karkashin tsohuwar jam’iyyar NRC, Alhaji Bashir Usman Tofa da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Kabiru Ibrahim Gaya da sakataren tsohuwar ANPP, Alhaji Rabi’u Bako da sauransu, suka ziyarci Gwamna Rabi’u Kwankwaso a gidan gwamnati, inda suka bayyana shi a matsayin jagoran jam’iyyar APC a jihar.
Sannan kuma a bangaren Malam Ibrahim Shekarau, magoya bayansa suna suka da kin amincewa da jagorancin jam’iyyar a karkashin Gwamna Rabi’u Musa
Kwankwaso, a wani  taron manema labarai da aka gudanar a gidan tsohon gwamnan. Shugaban tsohuwar jam’iyyar ta ANPP, Alhaji Sani Hashim Hotoro, ya bayyana cewa tawagar wadanda suka kai wa Gwamna Rabi’u Kwankwaso ziyara kuma suka bayyana shi a matsayin jagoran APC a Kano, sun je ne don kansu, ba da yawun bangaren ANPP ba.
Haka kuma, an kara jiyowa daga bakin mayakan baka na Jihar Kanon, wasu na ikirarin cewa muddin jagoran tafiyar (Janar Muhammadu Buhari) ya shigo Kano sai sun jefe shi, ko duka da yaga riga, kamar yadda suka yi wa daya daga cikin jagororin tafiyar, danbilki Kwamanda (wanda aka yi wa dukan tsiya a masallaci).
Anya kuwa wadannan duk ba su ishi shugabannin jam’iyyar APC ishara a kan su sasanta jama’arsu ba? Shin wannan ba matsala ba ce wadda za ta iya ba jam’iyyar PDP damar shigo da wasu ’yayanta  cikin jam’iyyar ta APC don ta cimma burinta na ci gaba da darewa kan madafun iko a 2015? Shi fa yaki dan zamba ne.
Tun daga kan jagoran tafiya, Janar Muhammadu Buhari da shugabannin jam’iyya da mabiya da masu son ci gaban kasarmu, ya zame mana wajibi mu bayar da shawarar bin duk wata hanya da za ta kawo ci gaban jam’iyyar APC. Domin muddin muka bar damar da muke da ita, muka yi watsi da ita, wallahi sai Allah Ya tambaye mu a kan yadda muke tafiyar da al’amurammu.
Gaskiyar magana ita ce, dole mu cire jin haushin wani a zukatanmu. Dole mu yafe wa junanmu a kan laifin da muka aikata wa junanmu, wanda muka sani da wanda ma ba mu sani ba. Dole mu sanya ci gaban al’umma a gabanmu, ba ci gaban kanmu ko wani bangare ba. Sannan mu yawaita addu’ar Allah Ya kawar da Shaidan da dangoginsa a tsakaninmu.
Ta haka ne Allah zai dubi lamuranmu, sannan Ya biya mana bukatunmu.
Masu hikimar magana na cewa, icce tun yana danye ake tankwasa shi. Sun kuma kara da cewa, gyara kayanka ba ya zama sauke mu raba!