✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Nan da wata 6 za mu gama aikin titin Kano-Kaduna —Julius Berger

A 2017 Gwamnatin Tarayya ta ba wa Julius Berger aikin gyaran hanyar da wa'adin wata 36.

Gwamnatin Tarayya ta ba da tabbacin kafin karshen shekarar da muke ciki za a kammala aikin gyaran babban titin da ya taso daga Kano zuwa Kaduna.

Daraktan Manyan Tituna, Ginawa da Gyaran su a Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Tarayya, Injiniya Folorunso Esan, ya ce aikin na tafiya yadda aka tsara, da zarar an kammala kuma za a koma kan bangaren Abuja zuwa Kaduna.

A 2017 Gwamnatin Tarayya ta ba wa kamfanin Julius Berger aikin gyaran hanyar Abuja zuwa Kano mai nisan Kilomita 375, da wa’adin wata 36.

Ba a fara aikin ba sai a 2018, kuma ba ya tafiya da sauri, lamarin da ya haifar da kokwanto game da yiwuwar kammalawa yadda aka tsara.

A ziyarar gani da ido d aya kai, Injiniya Esan ya bayyana kwarin gwiwa cewa zuwa 2023 za a iya amfani babban titin gaba daya, domin aiki ya yi nisa a kowane bangare.

“Yanayin tafiyar aikin ya gamsar kuma za a kammala kafin karshen shekara, abin da kawai zai rage shi ne bangaren daga Abuja zuwa Kaduna.”

Da aka tambaye shi game da tafiyar hawainiyar aikin bangaren titin daga Kaduna zuwa Abuja, sai ya ce, “Ai aiki  daya ne, saboda haka idan ka kammala wani bangare ai abu daya ne; Idan muka kammala wanna bangaren, sai kuma mu koma kan wancan bangaren a lokaci guda.”

Da yake magana, manajan kamfanin Julisu Berger mai kula da aikin titin Kano zuwa Kaduna, Theo Scheepers, ya ce za a kammala aikin yadda aka tsara.

Ya ce a halin yanzu an kammala kashi 70 cikin 100 na aikin kuma motoci na iya amfani da kilomita 112 daga cikin kilomita 150 da aka kammala daga Kano zuwa Kaduna.