✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nan da shekarar 2020 kashi 80% na al’ummar Najeriya za su kasance masu mu’amala da bankuna

Fassarar Bashir Yahuza Malumfashi da Isyaku Muhammed  da Jamilu Adamu A shekarar 2012 Najeriya ta kaddamar da shirin  fadakar da kan al’ummar Najeriya dangane da mu’amala…

Fassarar Bashir Yahuza Malumfashi da Isyaku Muhammed  da Jamilu Adamu

A shekarar 2012 Najeriya ta kaddamar da shirin  fadakar da kan al’ummar Najeriya dangane da mu’amala da bankuna wajen tafiyar da al’amuran kudi, inda aka kudurta cewa nan da shekara 2020 za a samu kashi 80 cikin 100 na al’ummar Najeriya da suke mu’amala da bankuna. Zuwa yanzu dai saura shekara daya ta rage a kai ga cimma wannan kudiri. Shin wadanne hanyoyi da hikimomi aka bi domin ganin an cimma nasara? Wakilinmu ya bibiyi al’amarin.

Wani bincike da Cibiyar Al’amuran Kudi ta EFInA ta gudanar a shekarar 2017, ya gano cewa kimanin kashi 38.8 na al’ummar Nijeriya ba su mu’amala da bankuna a harkokinsu na kudi. Wannan adadi ya ragu daga adadin mutanen da aka samu a shekarar 2016, inda ake da kashi 41.6 cikin 100.

Haka, wani bayanin kididdiga da aka samu daga Mataimakin Darakta a Babban Bankin Najeriya (CBN), Adedeji Adebisi ya nuna cewa adadin ’yan Najeriya miliyan 40.1 ba su mu’amala da bankuna a harkokinsu na kudi, a yayin da miliyan 56.3 ke mu’amala da bankuna a harkokinsu a Najeriya, wanda haka ke nuna cewa, an samu kashi 58.4 cikin 100 ke nan da ke mu’amala ta bankuna.

Idan aka dubi wannan karin adadi da aka samu, za a iya cewa an samu ci gaba amma duk da haka akwai sauran aiki, idan ana son cimma wancan adadi da aka kudirta zuwa shekarar 2020. Cibiyoyin kudi, kamar Babban Bankin Najeriya da Hukumar Inshora ta Kasa da Hukumar Lamuni da Jingina ta Kasa, duk suna sane da irin babban aikin da ke gabansu, na ganin an cimma nasara a shekarar 2020, dangane da kudirin samun kashi 80 cikin 100 na al’ummar Najeriya da za su kasance cikin mu’amala da bankuna a harkokinsu na kudi.

Dukan wadannan hukumomi, ba su nade hannuwansu ba, sun shiga aikin fadakarwa da wayar da kan al’umma dangane da amfanin mu’amala da bankuna a harkokinsu na kudi na yau da kullum, kamar yadda zamani ya kawo. Wadansu ma suna shiga makarantu, kasuwanni, wuraren tattaruwar al’umma da sauransu. Wannan kuma ya hada har da yekuwa a kafafen watsa labarai, inda ake sanar da talakawa cewa lallai akwai amfani wajen mu’amala da bankuna, domin akwai kudade da yawa da ake juyawa a wajen banki da suka kamata a rika amfani da su a bankuna, yadda za su rika amfanar al’umma gaba daya.

An ba da misalin yadda Babban Bankin Najeriya ya dauki wasu matakai masu dama a shekarun baya, wadanda suka taimaka wajen kara adadin mutanen da suke mu’amala da bankuna a Najeriya. Wasu daga cikin irin wadannan matakai sun hada da, ejan-ejan da ke fadakar da mutane dangane da sharuddodin mu’amala da bankuna da kuma samar da dillalai da suke gudanar da ayyukan banki a karkara a madadin bankunan na ainihi a ko’ina a Najeriya.

Haka kuma, yadda aka kaddamar da wasu harkokin banki na musamman a zamanance ta hanyar Intanet ma ya taimaka. Wannan na nufin yadda ake saye-da-sayarwa ta hanyoyin cibiyoyi da kasuwannin intanet da sauransu.

Haka kuma, a bara Babban Bankin Najeriya ya kaddamar da wani tsari na musamman da ya rika jawo hankalin al’umma dangane da muhimmanci su shiga a dama da su wajen mu’amala da bankuna a harkokinsu na kudi. Wannan shiri kuwa ya rika fadakar da al’umma irin kariyar da za su rika samu ta fuskar mu’amala da bankuna. Don haka Babban Bankin Najeriya ya yi amanna cewa,  sakamakon namijin kokarin da ake yi na fadakarwa kan wannan tsari a shekara biyu da suka gabata, za a iya cimma nasarar samun kashi 80 cikin 100 na al’ummar Najeriya da za su shiga cikin tsarin mu’amala da bankuna a harkokinsu na kudi, nan da shekarar 2020.

Domin a kara himma tare da nanata muhimmancin ilimantarwa game da wannan shiri, Babban Bankin Najeriya ya shirya gudanar da wani taron bita domin ilimantar da al’umma a Abuja. Ana da yakinin wannan taro zai fadakar, ya ilimantar da al’umma muhimmancin mu’amala da bankuna a harkokinsu na kudi.

A lokacin da yake jawabi a wajen taron, Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele ya ce muhimmancin fadakar da al’umma game da amfanin mu’amala da bankuna na da girma sosai. Muhimmanci da alfanun haka, inji shi, sun hada da karfafa harkokin saye-da-sayarwa a tsakanin ’yan kasuwa da masu saye da kuma ba al’umma damar zabin irin abin da suke bukata a bankuna da sauran cibiyoyin kudi.

Barazanar da ke tattare da karbar rancen kudade, wannan zai iya hana daidaita hada-hadar kudaden abin da ake sayarwa, wanda hakan zai iya kawo gasa a tsakanin cibiyoyin kudade don ingancin abin da ake sayarwa da kuma hanyar habbaka hanyoyin hada-hadar kudade, yayin da abokan hulda za su kara neman hajar da suke bukata a kasuwanni ta amfani da tsarin hada-hadar kudaden.

Mista Emefiele, wanda ya bayyana haka ta bakin Mataimakiyar Gwamnan CBN, Misis A’isha Ahmad, ya ce karancin wayar da kai kan hada-hadar kudade da ilimi da kuma natsuwar da abokin hulda ke da shi kan harkar, na daga cikin abin da ke kawo musu barazana, don haka sai mun yi da gaske wajen bin matakan samun nasarar shirin.

“A yau tsarin hada-hadar kudade na samun tsaiko daga ci gaban fasaha. Sababbin na’urorin sadarwa na zamani na kara bullowa, yayin da Intanet ke rudar abokan hulda wajen shawarar abin da suke son saya, sanadiyyar ci gaban da ake samu ta hanyar amfani da kasuwanci ta na’ura.

Misali a shekarar 2017 a tsarin bankuna biliyan 1.4 na kasuwancin na’ura ana ba shi darajar Naira tiriliyan 97.4  kuma ana amfani da shi a maimakon kasuwanci miliyan 869, yayin da darajarsa ta kai Naira tiriliyan 69.1 kamar yadda rahoto ya sanar a shekarar 2016.

A cewar Mista Emefiele, “A wannan ci gaban babu makawa ya dace da shirin, akwai alamar nasara a tsarin hadahadar kudaden kuma ana fatan zai taimaka wajen kokarin da ake yi duk da yake yana tattare da kalubale, wasu daga ciki su ne: sirrin tsarin da tsaronsa, bukatuwar sirri da tsaron bayanai na abokan hulda: bayyana sabuwar hanyar aikata laifuka, wanda akwai bukatar masu fada aji da su zage damtse; abokan hulda na samun bayanai da dama wanda hakan na iya sa su, su yi aiki da bayanan bogin da ake ta yada wa.

Gwamnan babban banki CBN ya ce, “Bukatarmu ita ce tabbatar da sahihanci hada-hadar kudade da samun ingantattun bayanai hakan zai magance matsalolin da shirin zai fuskanta da bunkasa hada-hadar kudaden da ake yi da abokan hulda da rashin bayanai ko kuma fahimtar harkokin da kuma sanin fargabar da ke ciki. Bayyanar hakan yana da matukar muhimmanci.

Gwamnan ya ce, ilimin hada-hadar kudade da kare martabar abokan hulda bai taba zama mana barazana ba tare hadin gwiwar masu ruwa-da-tsaki, don haka ya zama dole Najeriya ta yi nasara a kan shirin hada-hadar kudaden da ta sa a gaba.

Gwamnan CBN a taron da suka kaddamar sun sanar da sababbin hanyoyi da za a gudanar da hada-hadar kudade wadanda suka hada da:

(a) CBN ya kaddamar da dokokin da za su kare biyan lasisin bankuna wajen kokarin da suke yi ta  hanyar fasaha, hakan zai bunkasa hada-hadar kudaden da kuma sake habaka bullo da hanyoyin gudanar mu’amala da kudade ga wadanda ba su da asusun ajiya a bankuna da kuma sauran jama’ar da ba sa cikin tsarin.

Ana tsammanin hakan zai kawo wa shirin bunkasar  wadanda ke cikin tsarin kasuwanci, fasahar sadarwa a harkar da wasu sababbin hanyoyi da za su bunkasa harkar ajiya da biyan kudade da maido da kudaden da aka ranta na kananan masana’antu da kuma kananan ’yan kasuwa.

(b) Bankin kuma yana kokarin horar da masu amfani da tsarin  tare da hadin gwiwar kwamitin bankuna da hukumar da ke  raba rancen ayyukan noma ‘Nigeria Incentibe-Based Risk Sharing System for Agricultural Lending (NIRSAL),’ da hukumar rarraba wasiku NIPOST, kaddamar da kananan bankunan da ke bayar da rance, ‘Micro Finance Bank,’ duk za su bunkasa bayar da rancen kudade, wajen samar da kudade ga kananan masana’antu da kuma wasu kungiyoyin da ba sa ajiyar kudade a banki, bankunan MFB za su ci gaba da jan ragamar harkokin mu’amala da kudade da hukumar NIPOST a kananan hukumomi 774 da ake da su a Najeriya, za su zama wata hanya na biyan kudaden da kuma bin diddigin asusun ajiya, misali kamar shirin bayar da rancen kudi na ‘Anchor Borrowers fund’ da asusun kananan masana’antu da sauransu ga manoma da kuma kananan masana’antun da suke karkara,

A jawabin Daraktan sashen kare abokan hulda na CBN, Mista Kofo Salam-Alada, ya ce, duk da nasarorin da aka samu wajen gyara bangaren harkokin kudade, har yanzu akwai sauran kalubale. Manyan daga cikin wadannan kalubalen sun hada da, “rashin wayewa da ilimin harkokin kudade da kuma rashin tabbas da aminci a bangaren,” inji shi.

Ya ce za a gyara lamarin ne kawai ta hanyar wayar wa mutane kai da kuma shirye-shiryen kare abokan hulda, “Idan har ba a lura da bukatun abokon hulda ba- wato idan ya kasance suna yawan samun matsaloli kuma ba a magance musu su, dole su rika gajiya da bangaren. Kuma wannan zai rika shafar bangaren, wanda hakan ka iya jawo wa bangaren baki daya matsala,” inji shi.

Kuma ya ce Babban Bankin Najeriya na kokarin ganin cewa ya magance matsalolin ta hanyar shirye-shiryensa na wayar da kan al’umma, “Yanzu haka mun hada takardu biyu domin wadannan shirye-shirye. Wato Wayar da kan al’umma na kasa a karkashin shirin National Financial Literacy Framework (NFLF) da Financial Education Strategy (FES),” inji shi.

Ya ce tun da aka assasa bangaren kula da bukatan abokan hulda (CPD), an fitar da takardu da dama daga bangaren wadanda suka kunshi sashen taimako na Helpdesk wanda aka yi a watan Agustan shekarar 2011 da Consumer Protection Framework (CPF). Shi shirin CPF din yana da matakai uku ne, wato bangaren lura da tsara kasuwanci da bangaren amsa koke-koken al’umma da bangaren wayar da kai. Haka kuma a karkashin shirin, an an samu damar dawo da kimanin Naira biliyan 68 ga abokan hulda.

Mahalarta taron duk sun amince a kan amfanin hada hannu a tsakanin masu ruwa-da-tsaki a bangaren idan har ana so a cimma sauran kashi 20 na shirin a shekarar 2020 da aka tsara.

Da yake jawabi a wajen taron, Manajan Daraktan Bankin Ja’iz, Malam Hassan Usman ya ce bankin ya shiga cikin tsarin hada hannu da duk masu ruwa-da-tsaki. Ya ce bankinsu ya dade a cikin tsarin hada hannu da masu ruwa-da-tsaki da hanyar amfani da kimiyyar zamani wajen kaiwa ga wuraren da babu banki.

“Muna ayyuka a kuyuka a Katsina inda muka gana da mata masu sayar da kosai da masu fura da nono da sauransu domin ganin yadda za mu tallafa musu. Mun je ne ba domin mu samu wadanda za su sanya kudi a bankinmu ba, kawai muna so mu tallafa musu da kananan basussuka da za su yi amfani wajen samun kudi. Burinmu shi ne mu tallafa wa irin wadannan matan da suke zaune a kauyuka da birane domin fadada kasuwancinsu,” inji shi.