✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nan da shekara uku APC za ta wargaje – Maina Waziri

Tsohon Ministan ’Yan Sanda kuma dan takarar Gwamnan Jihar Yobe a karkashin Jam’iYyar PDP Alhaji Adamu Maina Waziri a zantawarsa da Aminiya ya ce, nan…

Tsohon Ministan ’Yan Sanda kuma dan takarar Gwamnan Jihar Yobe a karkashin Jam’iYyar PDP Alhaji Adamu Maina Waziri a zantawarsa da Aminiya ya ce, nan da shekara shida Jam’iyyar APC za ta wargaje, kuma ya ce har yanzu ’yan Najeriya ba su ga wani canji ba a mulkin Muhammadu Buhara saboda haka sai ya ba wa gwamnatin wata shida da ta kawo canji a kasar nan ko kuwa ta fuskanci adawa mai tsanani daga Jam’iYyar PDP:

Aminiya: An samu rikicin shugabanci a jam’iyyarku ta PDP tun faduwarku zaben bana. Ko me ya janyo hakan?
Maina Waziri: Zan fara ne da yin matashiya a kan cewa ne dan Jihar Yobe ne da muka shiga zabe sau hudu amma ba mu yi nasara ba muna hamayya wadda ita ce a yanzu PDP ta samu kanta a kasa baki daya.  A duk lokacin da aka shiga zabe aka fadi babbar masifa ce gaba daya jam’iyya takan birkice, za a samu mutanen da suke barin jam’iyya sakamakon faduwa zabe. Za a samu mutanen da jam’iyyar da ta yi nasara ta saye su. Suka yi zagon kasa, za a samu mutane da za su ce sun bar ma siyasa baki daya. Wannan hali na kaka-ni-ka-yi ne Jam’iyyar PDP ta shiga a Najeriya, saboda haka wannan abu da ya faru ya zama darasi ga mutane. Amma akwai takaici wanda har yanzu mutane ba su fahimci zurfin asarar gwamnati ko gwamnatocin da muka yi a kasa da jihohi ba.  Domin mutumin da ya saba da mulki na tsawon shekara 16, nafsi ma ya ce a tausaya mana amma har yanzu mutane ba su fahimta ba, idan tafiya ta yi tafiya za mu fahimta. A yanzu mutane da yawa suna barin Jam’iyyar PDP suna komawa APC saboda Jam’iyyar APC har yanzu budurwa ce ba ta fara kura-kurai ba, wadanda dole ne ta yi a mulkin kasa kamar Najeriya.
A lokacin da ta fara a sannan ne za mu fara hamayya da gwamnatin domin za mu samu abin fada, saboda mun ji ko mun gani. Duk da cewa muna fatan kada gwamnatin ta yi kura-kuran da jam’yyarmu ta yi har ta kai ga mun yi asarar gwamnati bayan shekara 16.
Aminiya: Wasu na ganin kura-kuran dai Jam’iyyar PDP na nan na yi domin har yanzu ba ta da shugaba na kasa kuma babu yadda za a yi jam’iyya ta yi tafiya ba tare da shugaba ba, me z aka ce?
Maina Waziri: A lokacin da tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Alhaji Adamu Mu’azu ya bayar da takardar barin kujerarsa Kwamitin Dattawan Jam’iyyar PDP da Kwamitin Zartarwa sun amince da takardar da kuma cewa za a saka wani ya yi rikon shugabancinta na wata uku. Bayan nan sai a nemo wani shugaban kuma wa’adin zai kare ne a karshen watan nan na Agusta, saboda haka ina tabbatar maka cewa akwai abubuwan da ke faruwa a kasa domin samun madadin Adamu Mu’azu daga shiyyar Arewa maso Gabas. Saboda haka idan aka dan saurara mana za mu samu kammala wannan aiki duk da cewa wadanda suka samu suka dare shugabancin jam’iyyar akwai alamun ba sa son. Amma wannan ra’ayi ne na wasu mutane ’yan kalilan domin babu yadda za a yi PDP ta farfado a Najeriya in ba an samu shugabanta dan Arewa ba ne, in kuma ba a samu dan takara dan Arewa ba. Domin ’yan Arewa ne da ba sa san tsohon Shugaba Jonathan ya dawo kan mulki suka taimaka aka zabi Shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Aminiya: A bayaninka ka nuna babu yadda za a yi Jam’iyyar PDP ta farfado daga kayen da ta sha a zabe sai shugabanta ya zama dan Arewa ta kuma tsayar dan takara daga Arewa. Ke nan kun dawo da batun karba-karba ke nan?
Maina Waziri: Ai PDP ita ce ta haifi karba-karba domin ba ya cikin dokar kasar nan. Amma yana cikin dabaru na cin zabe da muka ayyana wa kanmu ’yan PDP tun daga lokacin da muka kirkiro ta. Cewar siyasa, siyasa ce amma siyasar ta fi amfani idan aka ci zabe aka samu biyan bukata. Tun 1999 ba kawai ana neman Shugaban kasa ba ne, amma ana neman Shugaban kasar da zai samu sukunin da zai dawo da zamantakewa da zaman lafiya a kasar. Saboda haka ne muka amince mu dakushe karfinmu mu bai wa dan Kudu ya yi shugabancin shekara takwas, bayan nan sai ya dawo Arewa. Amma sai Allah Ya tafiyar da lamarin inda aka samu akasi marigayi Umaru ’Yar’aduwa bai karasa shekara hudu ba. Shi kuma wannan dan Kudun da ya hau duk da gatan da aka yi masa sai ya saba abin. Ina kuma san in nanata cewa Malam Adamu Ciroma ya yi yunkuri inda ya ce a shekarar 2011 a bar Arewa ta kammala shekarunta. Idan kuwa ba a bari ba, abin da zai biyo baya ba za mu ji dadi ba. Kuma ’yan kasar nan muka yi biris da maganarsa. Bayan kammala shekara hudu abin da ya kamata PDP ta yi da shi Shugaban kasar a shekarar 2015 sai a tsayar da dan Arewa amma sai muka dauki wuka muka daba wa kanmu har muka yi asarar gwamnati.
Aminiya: Ka ce Jam’iyyar PDP na cikin rudu, to me ya sa kuka makale a jam’iyyar kuka ki komawa APC?
Maina Waziri: Ai su ma wadanda suka karba sun yi rudun shekara 16, kafin Allah Ya taimake su suka tattara kansu har suka samu saboda shi ne dimokuradiyya. Ma’anar dimokuradiyya fa ita ce za a yi zabe wani ya yi nasara. Wanda ya yi nasarar nan sai da ya kada wani. Kuma kafin a samu mai nasara sai an samu mara nasara. Mu a yanzu a matsayinmu na ’yan siyasa kuma da muka yarda da ikon Allah muna ganin wannan dimokuradiyya ce an shiga zabe mun fadi wani ya ci. Mun kuma tabbata cewa za mu sake shiga zabe wani zai fadi mu kuma mu ci.
Aminiya: Kuna ganin nan gaba PDP za ta sake cin zabe duk da kayen da ta sha a zaben 2015?
Maina Waziri: Zabe mai zuwa ai da nisa kuma ba zai yiwu a ce dole sai PDP ta karbi ragamar mulki ba, wadanda suka karba yanzu ai hadaka ne fa. Hadin gambiza ne wanda ina tabbatar maka cewa daga nan zuwa shekara uku za ta wargaje.
Aminiya: Jihar Yobe na daya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro, amma ba ku yi fushi da gwamnatin PDP ba duk da matsalar tsaron da ta ki ci ta ki cinyewa a yankin Arewa maso Gabas?
Maina Waziri: Matsalar rashin tsaro akwai abin da ya haddasa ta. Ni dan Jihar Yobe ne amma ni matsalar tsaro ba ita ce matsalar ba. Rashin shugabanci nagari da aka yi shekara 16 ya haifar da rashin tsaron. Allah bai albarkaci Jihar Yobe da shugabanni nagari ba a tsawon shekara 16 da suka wuce ba, inda a yau a bangarorin rayuwa jihar ce kashin baya. Duk kasar da ke da irin wannan a yanzu za ta fuskanci rashin tsaro, za ta fuskanci bala’o’i irir-iri. Domin nafsi ne ya ce idan shugabanni suka zamo azzalumai Allah zai jarabci al’ummar kasar da masifu iri-iri, wannan ne ya same mu a Jihar Yobe.
Aminiya: Ba ka ganin za su dauka kana tsokanansu ne bayan suna iya bakin kokarinsu a jihar?
Maina Waziri: Ai ba tsokana ba ne abu ne da ba yau na fara fadi ba, kuma idan ba an samu canji na shugabanni nagari ba, wadanda  ba azzalumai ba, ba marasa imani ba, har abada kasa ba za ta ci gaba ba. Idan an samu shugabanni nagari kuwa al’umma za su samu saukin rayuwa, kuma za su ji dadi. Wannan kuma ba maganar kasar Musulmi ne kawai ba, idan ka je kasashen da ba na Musulmi ba kamar Turai da Amurka da sauransu, za ka ga shugabanninsu ba sa karan-tsaye ko zalunci da rashin gaskiya kamar yadda shugabanni ke yi a nan kasar. A can idan suka yi ba za su kwana biyu ba za a cire su, amma a nan mu duk da mun san Allah mun kuma san shugabanci amma har yanzu muna jiran Mahadi ya bayyana domin mu shiga taitayinmu wanda kuma ba zai yiwu ba.
Aminiya: Me za ka ce game da gwamnatin Muhammadu Buhari?
Maina Waziri: Har yanzu ba mu ga canji ba, ba mu gan shi a kasa ba. Muna jira muna son yi masa adalci tare da yi masa fatan alheri. Na biyu mun ba shi wata shida zuwa karshen shekara ke nan, daga nan za mu yi cara.