Gwamnatin Tarayya ta ce za a ci gaba da sufurin jirgin kasan Abuja-Kaduna a cikin watan Nuwamba da muke ciki.
Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a yayin da yake jawabi kan ayyuka ma’akatar.
- NDLEA ta kama makaho dan Nijar da safarar miyagun kwayoyi
- Gara na mutu ga in goyi bayan Atiku —Ortom
Wannan na zuwa ne wata guda bayan Gwamnatin Tarayya ta ceto ragowar fasinjojin da ’yan ta’adda suka yi garkuwa da su a jirgin kasan a ranar 5 ga Oktoba, 2022.
Ministan ya bayyana cewa an tanadi matakan tsaro na tsawon awa 24 ga sufurin jirgin kasan, wanda wata bakwai ke nan da dakatar da shi.
A cewarsa, ma’aiakatar ta dauki darasi gada abin da ya faru a harin da aka aka kai wa jirgin kasan a baya, wanda ya yi sanadin dakatar da sufurin.
A ranar 28 ga Maris 2022 ne Gwmnatin Tarayya ta dakatar da sufurin jirgin kasan Abuja-Kaduna, bayan ’yan ta’adda sun kai masa harin bom suka kashe mutum 10 tare da sace wasu 60.