✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Nan ba da jimawa ba jirgin kasan Kano Zuwa Legas zai dawo aiki – NRC

NRC ta ce ba za ta iya kiyasta asarar da ta tafka sakamakon dakatar da sufurin na Kano zuwa Legas ba.

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Kasa ta Najeriya (NRC) ta ce ta kammala shirye-shiryen dawo da ayyukan jirgin kasa daga Kano Zuwa Legas wanda annobar COVID-19 ta jawo dakatarwa a baya.

Jami’in shiyya na hukamar a Legas, Injiniya Jerry Oche ne ya tabbatar da haka yayin zantawarsa da ’yan jarida a Legas, jim kadan da karbar kyautar jami’in shiyya na hukumar mafi kwazo, inda ya ce tuni shirye-shirye suka kammala wajen dawo da ayyukan jirgin.

A cewarsa, hukumar za ta fara aiki ne da jigilar wasu bututan ruwa kimanin 6,000 mallakin Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Kaduna zuwa Zariya.

Aminiya ta gano cewa a cikin ’yan kwanakin nan ne dai NRC ta tura injiniyoyinta domin su gyara sassan da suka lalace a kan layin dogon mai tsawon kilomita 1,126 daga Kano zuwa Legas.

Mista Oceh ya ce hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen dawo da aikin domin kaucewa sake lalata layukan dogon wadanda ya ce sakamakon dakatar da aiki tuni wasu mutane suka fara lalatawa.

Sai dai ya ce tuni aka cafke irin wadannan mutanen da dama kuma yanzu haka suna hannun Ofishin ’Yan Sanda na Hukumar domin su girbi abin da suka shuka.

Jami’in ya ce NRC ba za ta iya kiyasta asarar da ta tafka sakamakon dakatar da aikin sufurin na Kano zuwa Legas ba.