✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta hadu da Ajantina a wasan sada zumunta

A shirye-shiryen tunkarar Gasar Cin Kofin duniya da zai gudana a badi a Rasha, Najeriya ta tuntubi kasar Ajantina kuma tuni kasashen biyu suka amince…

A shirye-shiryen tunkarar Gasar Cin Kofin duniya da zai gudana a badi a Rasha, Najeriya ta tuntubi kasar Ajantina kuma tuni kasashen biyu suka amince su yi wasan sada zumunta a watan gobe.

Kamar yadda Sakatare-Janar na Hukumar NFF Mohammed Sanusi ya bayyana, ya ce Ajantina ta amince da tayin da Najeriya ta yi mata na buga wasan sada zumunta kuma ana sa ran wasan zai gudana ne a ranar Talata 14 ga watan gobe a filin wasa na Krasodar da ke kasar Rasha.

Wannan wasan tamkar gwaji ne a shirye-shiryen tunkarar gasar cin kofin duniya ga kasashen biyu.

Rabon da kasashen biyu su hadu tun a ranar 25 ga Yunin 2014 a Gasar Cin Kofin Duniya da ya gudana a Brazil inda Ajantina ta lallasa Najeriya da ci 3-2.  A wasan, Ahmed Musa ne ya zura wa Najeriya dukkan kwallayen biyu a ragar Ajantina.

“Mun tattauna da Ajantina a game da yin wasan sada zumunta kuma tuni kasar ta amince  don haka muna sa ran wasan zai gudana ne a Rasha a ranar 14 ga watan gobe”, inji Mohammed Sanusi.