✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya za ta daina sayo fetur daga kasar waje a 2023 —NNPC

NNPC ya ce a tsakiyar shekarar 2023 za a daina shigo da tataccen mai Najeriya daga kasashen waje

Shugaban Kamfanin Mai na Najeriya (NNPC) Mele Kyari, ya ce kasar za ta daina shigo da dan tataccen mai daga kasashen waje a shekarar 2023 mai kamawa.

Ya ce za a daina shigo da tattacen mai ne da zarar matatar mai da attajirin Afirka, Aliko Dangote ke ginawa ta fara aiki a tsakiyar 2023.

Shugaban na NNPC ya bayyana haka ne Fadar Shugaban Kasa a lokacin jawabin da Sashen Yada Labarai na fadar ya shirya karo na 49.

A shekarar 1957 aka fara hako man fetur a Najeriya, wanda a 1960 ta fara fitarwa zuwa kasuwanni duniya.

Amma bayan shekaru kasar ta koma amfani da kaso mai tsoka na kudaden da take samu daga danyen manta wajen sayo tattacensa daga waje domin amfani da shi a cikin gida.

Hakan kuwa ta faru ne sakomakon shekaru da aka shafe na rashin zuba jari yadda ya kamata gami da cuwa-cuwa da suka yi wa bangaren katutu.

Wannan ne ya kara wa tattalin arzikin kasar nauyi gami da hana gwamnatin kasar damar amfani da kudaden da take samu daga sayar da danyen mai wajen gudanar da ayyukan inganta rayuwar jama’ar kasar yadda ya kamata.

Kwararru a fannin harkar mai sun bayyana bayanin na Mele Kyari a matsayin albishir da zai taimaka wajen kawo karshen bayar da tallafin mai da ke lakume wa gwamnati bilyoyin Naira, wanda ba abu ne mai dorewa ba.

Biyan tallafin man da gwamnati ke yi domin saukaka farashinsa ga jama’ar Najeriya dai na tattare da rudani da zargin almundahana, baya ga tilasta wa gwamnati ciyo bashin tiriliyoyin Naira.

Fasahar zamani za ta maganci matsalar makamashi

Kyari, ya fara aikin matatar Dangone zai sa a samu karin karfin tace danyen mai a cikin gida, wanda bayyana cewa zai kawo karshen shigo da tataccen mai daga waje.

A cewarsa, zuwa tsakiyar shekarar 2023, Najeriya za ta iya wadata kanta da tataccen man da take bukata, musamman idan aka kammala gyaran matatun gwamnati da kuma matatar Dangote wadda Gwamnatin Tarayya da ke kashi 20 cikin 100 na hannun jari.

ya ce: “NNPC na da kashi 20% na hannun jari a Matatar Dangote kuma mu ke da hakkin farko na bai wa matatar danyen mai domin ya tace.

“Amma nan gaba, saboda da cigaban da ake samu a bangaren makamashi, za a kai lokacin da babu mai neman danyen mai ya saya; Shi ya sa muka fara tunanin nan da shekara 20 masu zuwa ganga 330,000 da man za mu rika sayarwa a rana,” in ji shi.

Jarin da muka sa a matatar Dangote ta ba mu galaba

Kyari ya ce hannun jarin da NNPC ke da shi a Matatar Dangote ya ba shi karin damar kashi 20 cikin 100 na duk abin da matatar ta samu.

“Muna sa ran ta fara aiki a farkon shekarar amma mun fi sakankancewa zuwa tsakiyar shekarar, kuma idan ta fara aiki za ta samar da tataccen mai fiye yadda aka saba domin tana da karfin samar da ganga 650,000 baya ga sauran fasahohin zamani.

“Hakan na nufin za a iya sama da lita miliyan 50 na fetur, saboda haka idan aka hada da man da mataatun gwamnati za su samar, zai kawar da batun shigo da mai daga waje a 2023.”

Ya kuma kara jaddada cewa gwamnati na yin abin da ya kamata domin farfado da matatunta da ke sassan Najeriya.

Masallatai da jami’an gwamnati na da hannu a satar mai

Shugaban Kamfanin Mai na NNPC, Mele Kyari, ya bayyana takaici bisa yadda satar danyen mai ke jawo wa Najeriya asarar kudaden shiga da ya kamata ta samu daga kasuwannin duniya.

Ya bayyana haka ne lokacin da ya bayyana cewa kamfanin ya bankado yadda masallatai da coci-coci da jami’an gwamnati ke da hannu a satar mai.

Ya nuna damuwar bisa girmar matsalar fasa bututan mai da ake yi da hadin bakin kungiyoyin addini da sauran mutane a yankunan da layin bututun ya wuce.

Mele Kyari ya bayyana cewa a wani wuri da tsawonsa bai wuci mita 200 ba, NNPP ta gano wurare 295 da barayin mai suka ja bututum mai.

Shugaban kamfanin a yi zargin cewa a wasu wuraren an janyo bututun mai ta barauniyar hanya zuwa masallatai da coci-coci.

Ya ce NNPC ya samu nasarar ce da taimakon da ya samu daga jami’an tsaro na ciki, bisa umarnin Babban Hafsan Tsaron Najeriya.

Ya bayyana takaici bisa yadda barayin man suke jawo wa Najeriya asarar makudan kudaden shiga da ya kamata ta samu daga kasuwannin duniya.

A cewarsa, kamfanin ba za ta yi kasa a gwiwa ba, kuma yana samun nasarori wajen magance matsalar satar danyen man ta watsu har a tsakanin shugabannin addini da kungiyoyin addini da sarakuna da jami’an gwamnati da sauran al’umma.

A cewarsa, kawo yanzu an kama kwalekwale masu gudu 30, kwalekwalen katako 170 da manyan motoci 37 daga hannun masu fasa bututun mai, kuma gwamnati ta dauki matakin kona su gaba daya.

An kuma cafke mutum 122, ciki har da wasu fitattun mutane a tsakanin watan Afrilu da Agusta, kuma an mika wasunsu ga Hukumar EFCC, mai yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa.

Daga: Sagir Kano Saleh, Muideen Olaniyi, Simon E. Sunday & Philip S. Clement