Gwamnatin Najeriya ta sanar da kara kuɗin mallakar takardar fasfo tafiye-tafiye da kashi 43%.
Hukumar Shige da Fice ta bayyana cewa an ƙara kuɗin mallakar fasfon a gida Najeriya ne kawai, bai shafi masu yi a kasashen waje ba.
Sanarwar da kakakin hukumar, Kenneth Udo, ya fitar ta ce takardar fasfo mai shafi 64 ya tashi daga N75,000 ya koma N100,000.
Fasfo mai shafuka 32 kuma an ƙara kudin mallakarsa daga Naira dubu 35 zuwa Naira dubu 50.
- Ɗan Sarkin Gobir da aka sace su tare ya kuɓuta daga hannun ’yan bindiga
- Satar doya ta sa an yi masa zindir a Abuja
Sanarwar ta ranar Laraba ta ce sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 1 ga watan Satumba, 2024.
A cewarsa, an ƙara kuɗin mallakar fasfo ɗin ne da sun kara ingancinsa da nagaratarsa.