Najeriya ta yi asarar Dala biliyan 5.9 sakamakon cutar daji a shekararar 2019, in ji wani rahoton Hukumar Lancet Oncology ta yankin Saharar Afirka.
Shugaban Hukumar, Farfesa Wil Ngwa ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja, yayin wani taro da hukumar ta shirya kan halin da cutar kansa ta jefa yankunan Saharar Afirka.
- Ambaliya ta ci mutum 3, wasu 50,000 sun rasa muhallansu a Kogi
- Kwastam ta kwace shinkafa da kayan N79m a Katsina
Da yake jawabi kan rahoton, shugaban ya ce baya ga Najeriya, kasar Angola ta kashe Dala biliyan 1.3, Aljeriya kuma Dala 2.6, Jamhuriyar Benin Dala 209.2, Bostwana Dala 500.6, sai Burkina Faso Dala milyan 270.6, duk a sandiyar cutar.
Ngwa ya ce cutar daji ta yi sanadiyar mace-mace a shekarar 2021 a Afirka fiye da COVID-19, kuma a 2022 karin yara sama da 28,000 da sun mutu sanadiyar cutar.
An yi hasashen cewa zuwa shekarar 2030 za a iya samun mutuwar mutane miliyan Daya a yankin Afirka sanadiyar kamuwa da cutar daji.
Haka kuma ya ce dole ne nahiyar Afirkta ta magance cutar kansa cikin gaggawa kamar yadda ta yi wa COVID-19.
Ya ce kalubalen da cutar kansa ta jefa yankunan Kudu da Hamadar Sahara a halin yanzu na da yawa, kuma akwai yiyuwa ya ta’azzara cikin sauri idan aka gaza daukar matakan hadin gwiwa tsakanin kasashe.
Ya ce ciwon daji a Afirka na da alaka da dadewar bayyanarta, da jinkirin gano ta a likitance, hadi da rashin samun maganinta.
A nasa bangaren tsohon Ministan Lafiya na Najeriya, Farfesa Isaac Adewole, ya ce akwai matakai daban-daban da Gwamnatin Tarayya ta ke dauka domin rage radadin cutar a Najeriya.