Shugaban Kamfanin Man Fetur na NNPC, Mele Kolo Kyari, ya ce daga watan Janairu zuwa yanzu Najeriya ta yi asarar dala biliyan 1.5 saboda ayyukan masu fasa bututun mai.
Kyari ya bayyana hakan ne yayin da ya bayyan a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Harkokin Man Fetur a ranar Alhamis.
- Mun dakatar da Rasha daga Hukumar Kare Hakkin Bil’adama —MDD
- Mutum miliyan daya za su yi aikin Hajji a bana —Saudiyya
Ya koka kan ayyukan tsageru masu fasa bututun man fetur da kuma masu matatun mai ba bisa ka’ida ba ke haifar wa Najeriya asarar makudan kudi.
“Ayyukan tsageru masu fasa bututun man fetur da kuma masu matatun mai ba bisa ka’ida ba ya janyo asarar dala biliyan daya da rabi na danyen mai daga watan Janairu zuwa yau.”
Mele Kyari ya ce bangaren man fetur na kasar na samar da mafi karancin danyen mai da ya kai ganga miliyan 1.49 a kowace rana sakamakon karuwar ayyukan barna da masu gudanar da matatun mai ba bisa ka’ida ba.