Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarain ci gaba da aiki da nakasassu domin tabbatar da ganin ana damawa da su kamar sauran jama’a.
Ministar Jinkai da Agajin da Bunkasa Rayuwa, Sadiya Umar-Farouq ce ta bayyana hakan a Abuja ranar Laraba yayin jawabi ga ’yan jarida domin bikin ranar alamomi da kuma ta kurame ta duniya mai taken ‘Tabbatar da ’yancin kurame’.
Ta ce ma’aikatar za ta tabbatar cewa ana damawa da dukkannin naksassu musamman a harkokin shugabanci ta hanyar cire duk wani abu da zai kawo musu tarnaki.
Daga nan sai ta yi kira ga ’yan Najeriya kan su koyi amfani da alamomin kurame domin a samu sauki wajen mu’amala da su.