✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta sanar da ranakun hutun Kirsimati da sabuwar shekara

Gwamnatin tarayyar  Najeriya ta sanar da ranakun 25 ga watan Disamba da 26 wato Laraba da Alhamis da kuma 1 ga Janairun 2020 a matsayin…

Gwamnatin tarayyar  Najeriya ta sanar da ranakun 25 ga watan Disamba da 26 wato Laraba da Alhamis da kuma 1 ga Janairun 2020 a matsayin hutun Kirsimati da kuma na sabuwar shekara.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da Barista Georgina Ehuriah ya fitar a madadin gwamnatin tarayya.

Sanarwar ta kara da cewa, Ministan ya taya Kiristoci da kuma ‘yan Najeriya murna da kuma yin kira da zauna lafiya yayin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.