✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta lallasa Saliyo da ci 2-1

Ana buga wasan ne don neman cancanta buga Kofin Nahiyar Afirka

Kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta lallasa takwararta ta Leone Stars ta kasar Saliyo da ci 2-1 a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.

An dai fafata wasan ne don neman gurbin cancanta buga Kofin Nahiyar Afirka (AFCON).

Dan wasa Jonathan Morsay ne ya ci kwallo ta farko a minti na 11 da fara wasan, amma dan wasan tsakiya da ke wasa a kungiyar Everton, Alex Iwobi ya sake jefa wa Najeriya kwallo ta biyu a minti na 16.

Da wannan nasarar dai, yanzu Najeriya ce ta biyu a rukunin ‘A’, inda take da maki uku daga wasa daya.

Kasar Gini Bisau ce dai a saman teburin rukunin su ma da maki uku, kodayake su kwallo biyar suka ci a wasan da suka doke Sao Tome and Principe, wanda aka tashi 5-1.