Kungiyar kwallon kafar Najeriya ta Super Eagles ta lallasa takwararta ta Leone Stars ta kasar Saliyo da ci 2-1 a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.
An dai fafata wasan ne don neman gurbin cancanta buga Kofin Nahiyar Afirka (AFCON).
- Sarkin Kwatarkwashi a Jihar Zamfara ya rasu
- Cutar Sankarau ta kashe mutum 100 a Jigawa, ta fara kurumtar da wasu
Dan wasa Jonathan Morsay ne ya ci kwallo ta farko a minti na 11 da fara wasan, amma dan wasan tsakiya da ke wasa a kungiyar Everton, Alex Iwobi ya sake jefa wa Najeriya kwallo ta biyu a minti na 16.
Da wannan nasarar dai, yanzu Najeriya ce ta biyu a rukunin ‘A’, inda take da maki uku daga wasa daya.
Kasar Gini Bisau ce dai a saman teburin rukunin su ma da maki uku, kodayake su kwallo biyar suka ci a wasan da suka doke Sao Tome and Principe, wanda aka tashi 5-1.