✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta lallasa Arjentina

Najeriya ta lallasa kasar Arjentina da ci hudu da biyu a wasan sada zumunta da ya wakana a Rasha. Da farko dai, qasar Arjentina ce…

Najeriya ta lallasa kasar Arjentina da ci hudu da biyu a wasan sada zumunta da ya wakana a Rasha.

Da farko dai, qasar Arjentina ce ta fara wasan da zafi-zafi, inda ta rika taka leda da nuna gwaninta har ta zura kwallaye biyu a ragar Najeriya.

Kwallon farko dai mai tsaron gidan Najeriya Daniel Akpeyi ne ya yi kuskure, inda ya kama kwallo a wajen layin 18, wanda hakan ya sa alkalin wasa ya busa bugun tazara. Wannan kuskuren ne ya yi sanadiyar kwallon farko inda Ever Banega ya jefa kwallon kai tsaye zuwa ragar Najeriya. Sannan kuma Sergio Aguero ya kara kwallo na biyu bayan ‘yan mintuna.

‘Yan wasan Najeriya dai sun kara kaimi matuka daga baya, inda suka zura kwallaye hudu.

Kelechi Iheanacho ne ya zura kwallo na daya a bugun tazara kafin a tafi hutun rabin lokaci. Sai kuma Alex Iwobi ya zura kwallo na biyu da na hudu, bayan Bryan Idowu ya zura na uku.

Iheanacho dai ya zura kwallo daya, kuma ya taimaka aka zura kwallaye biyu, sai kuma Alex Iwobi da ya zura kwallaye biyu su ne wadanda suka ki fi yin kokarin a wasan.

Sai kuma mai tsaron gidan da ya shigo bayan hutun rabin lokacin, Francis Izoho wanda ke bugawa kungiyar Depotivo na kasar. Wanda kuma ake ka sa ran da alamu an samo wanda zai iya maye gurbin Vincent Enyeama, idan har bai dawo ba.