Ministan Kimiyya da Fasaha da Kirkira, Adeleke Mamora, ya ce ma’aikatarsa ta kirkiro allurar rigakafin cutar Sikila da ta dafi irinsu na farko a Najeriya.
Ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Litinin, yayin da yake jawabi a kan taron bayyana nasarorin gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari karo na 10.
- Gwamnatin Borno ta fara shirin daukar sabbin malaman makaranta 3,000
- Jirage 30 za su debi ’yan Maroko zuwa kallon wasan kasar da Faransa
Ministan ya kuma ce ma’aikatat ta sami nasarar kirkiro maganin cutar Sikila daga ganyakai, saboda yawan masu cutar a Najeriya.
Adeleke ya kuma ce, “Mun kuma kirkiro maganin dafi da wanda yake hana yawan kiba.
“Ma’aikatar, ta hannun Hukumar Bunkasa Bincike kan Kayakkin Masana’antu ta Najeriya ta kuma kirkiro fasahar da ke kara yawan madarar da ake iya tatsa daga jikin saniya daga kimanin lita daya ko daya da rabi, zuwa sama da lita 15 a rana daya.
“Yanzu haka ita ma Hukumar Bunkasa Bincike kan Sararin Samaniya na aikin wani gini a sama wanda ake sa ran zai samar wa Najeriya kudaden shiga har kimanin Naira biliyan 30, ya inganta harkar yawon bude ido sannan ya samar da ayyukan yi na kai tsaye 5,000 da kuma na wuccin gadi kimanin 20,000.
“Muddin muka ci gaba da yadda muka faro yanzu a kan harkar bincike da kirkira, to tabbas Najeriya za ta yi gogayya da manyan kasashe a fannin masana’antu a duniya nan ba da jimawa ba.
“Amma muna bukatar karfafa gwiwa da da’a a matsayin ginshikan tabbatar da cewa wadannan mafarkan sun zama gaskiya,” inji Ministan.