Tsohon Shugaban Kasa, Cif Olusegun Obasanjo, ya yi korafin cewa Gwamnatin Najeriya ta ki ribatar sakamakon kidayar al’ummar kasar da aka gudanar a shekarar 2006.
Obasanjo ya bayyana hakan ne a Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun yayin da yake kira ga Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC), da ta gudanar da aikin kidaya mai tsafta da inganci a 2023.
- Yajin aikin ASUU: Kungiyoyi 47 sun shiga zanga-zangar NLC a Kaduna
- An bayyana sojojin rundunar tsaron shugaban kasa da aka kashe a Abuja
A cewar tsohon Shugaban Kasar, aiwatar da ingantacciyar kidaya ce zai taimaka wa kasar wajen samar da tsare-tsaren da ‘yan kasa za su ci moriya.
Bayanan Obasanjo na zuwa ne a Talatar nan yayin karbar bakuncin Shugaban NPC na kasa, Malam Nasir Kwarra da mukarrabansa da kuma wakilan Hukumar da ke Kula da Yawan Al’umma ta Majalisar Dinkin Duniya (UNFPA) a Najeriya.
Tsohon Shugaban Kasar ya ce, muddin NPC ta gudanar da shirin kidayar ’yan kasa mai inganci hakan zai taimaka wa kasa matuka wajen cigabanta da al’ummarta baki daya.
Ya ce, a duk tarihin Najeriya a zamanin mulkinsa a 2006 kadai aka taba gudanar da aikin kidaya ba tare da an samu tangarda ba, yana mai cewa, duk da haka Najeriya kidayar ba yadda ya kamata.
“Muna guje wa yin amfani da sakamakon kidayarmu, kamar yadda muke gudun addininmu da yarenmu.
“Sakamakon kidayar baya da muka guje wa tun a 2006, shi ya kamata ya jagorance mu wajen sanya iyaka a tsakanin mazabu,” inji Obasanjo.
Kazalika, Obasanjo ya ce rashin yin amfani da sakamakon kidayar bayan gudanar da ita barnar dukiyar kasa ce, don haka ya ce ya kamata a san da wannan domin sanin inda ake a yau.
A nasa jawabin, Malam Kwarra, ya yaba wa Obasanjo bisa nasarar da ya samu wajen gudanar da aikin kidaya a zamanin mulkinsa a 2006.
(NAN)