✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta kassara dangantakar diplomasiyyarta

Wata bukata da kasar Jordan ta mika wa Kwamitin Tsaro na Majalisar dinkin Duniya a madadin Palsdinawa tana neman a kawo karshen mamayar da Isra’ila…

Wata bukata da kasar Jordan ta mika wa Kwamitin Tsaro na Majalisar dinkin Duniya a madadin Palsdinawa tana neman a kawo karshen mamayar da Isra’ila ke yi wa kasar Palsdinu nan da shekarar 2017, ta gaza samun nasara ne, saboda ba ta samun isassun kuri’ar wakilan kwamitin don tsallake wannan siradi.

kasashe takwas wato – Faransa da Rasha da China da Luzembog da Ajentina da Jordan da Chile da shugabar kwamitin na karba-karba wato Chadi, sun jefa kuri’ar amincewa da bukatar. Amurka da Autireliya sun jefa kuri’ar rashin amincewa.
Har zuwa dab da za a kada kuri’ar a ranar Talatar makon jiya, jakadu suna sa ran bukatar za ta samu kuri’ar amincewa tara da ake nema. Amma sai Najeriya ta kaurace wa jefa kuri’ar, inda Jakadar Najeriya a Majalisar dinkin Duniya, Joy Ogwu ta nanata matsayin Amurka wajen cewa hanyar samun zaman lafiya ya dogara ne da “hanyar tattaunawa.”
kuri’a daya ta Najeriya kamar yadda ta saba kan wasu kudirorin Tarayyar Afirka (AU) na goyon bayan wadanda ake zalunta maimakon ’yan mamaya, irin yadda ya faru a lokacin mulkin nuna wariyar launin fata a Afirka ta Kudu na iya canja al’amura wajen amincewa da bukatar. Bukatar na neman kuri’a tara ne kawai; duk da cewa Amurka na iya hawa kujerar na ki. Amma sai Najeriya ta zabi abin kyamar da ya ceci Amurka daga aikata abin kunya na sai ta yi amfani da kujerar na ki kafin a samu warware batun mamayar Isra’ila da Paladinu cikin ruwan sanyi.
daya daga cikin mafiya tasirin kokarin da Kwamitin Sulhu na Majalisar dinkin Duniya ya yi shi ne, kudiri na 242 da kwamitin ya amince da shi ba hamayya a ranar 22 ga Nuwamban 1967, bayan yakin kwana shida da aka fafata tsakanin Isra’ila da Larabawa. Birtaniya ne ta gabatar da shi, kuma aka amince da shi a karkashin Babi na Shida na kudirin Majalisar dinkin Duniya.
Gabatarwar kudirin yana cewa: “Rashin amincewa da kwace yankin kasa ta hanyar yaki da bukatar da ke akwai ta kowace kasa a yankin ta zauna cikin kwanciyar hankali.”
Sakin Layi na daya na kudirin, “Ya tabbatar da cewa burin manufofin kudirin shi ne bukatar a yi adalci tare da samar da tabbataccen zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya, kuma hakan ya hada da aiwatar da manufofi masu zuwa: (i) Janye sojojin Isra’ila daga yankunan da ta mamaye a rikicin na baya-bayan nan; (ii) Kawo karshen dukkan da’awoyi ko mallakar kasa da girmamawa da amincewa da ’yanci da iyakoki da ’yancin siyasa kowace kasa da ke yankin da kuma ’yancinsu na su zauna lafiya a inda yankin da suke tare da amincewa da iyakokinsu da kuma daina yi musu barazana ko nuna karfi.” Zuwa shekarar 2013, Kwamitin Kare Hakkin dan Adam na Majalisar dinkin Duniya ya la’anci Isra’ila a cikin kudirorin 45, tun kafa shi a shekarar 2006. Majalisar ta kuma yanke karin wasu shawarwari da suke la’antar Isra’ila fiye da na sauran kasashen duniya gaba daya. Babban Taron Majalisar dinkin Duniya ya amince da kudurce-kudurce da dama yana cewa ‘dabarun dangantaka’ da Amurka ya karfafa Isra’ila ta rika daukar matakai masu zafi da tsare-tsaren fadada kasarta. Kuma an kira zaman Gaggawa na Babban Taron Majalisar ne bisa bukatar Kwamitin Tsaro lokacin da Amurka ta toshe yunkurin amincewa da sanya takunkumi ga Isra’ila. Don haka sanan ne cewa burin Amurka da kare bukatunta na cikin kasa ne ya sa take hana samun nasarar kudirin da ke neman sanya birki ga Isra’ila da dakile cin zali da rashin tausayi da tauye hakkin dan Adam da kasar ta Yahudawa take nuna wa Palasdinawa shekara da shekaru. Mene ne riba ko hikimar Najeriya na wannan canji kwatsam daga matsayinta na goyon bayan kudirorin AU da kungiyar kasashen Larabawa da kuma na kasashen ’Yan Ba Ruwanmu? Wasu bayanai sun ce, Firayi Ministan Isra’ila Binyamin Netanyahu da Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ne suka kira Shugaba Goodluck Jonathan ya canja shawara duk da irin alkawarin da Najeriya ta yi wakilan Palasdinu a Majalisar dinkin Duniya cewa Najeriyar za ta jefa kuri’ar goyon bayan kudirin. Alkawarin Najeriya da sanin mutuncita ya karfafa gwiwar Palasdinawan suka bugi kirjin cewa suna da tabbacin samun kuri’a tara da akebukata; sai dai a wannan muhimmin lokaci sai Najeriya ta kasa cika alawarainta. Wannan canjin matsayi abin kunya ne da zubar da mutunci da zai dada nuna Najeriya a matsayin wadda ba za a dogara da it aba a yankin Afirka. Akalla bayanai biyu sun ce kiran da Netanyahu da Kerry suka yi wa Jonathan ne ya jawo sauyin ra’ayin. Ina cijewa da dakewar da aka san Najeriya da shi? Mene ne gudunmawar Isra’ila wajen yaki da hare-hare da Najeriya ke yi, hujjar da aka ambata a matsayin mai yiwuwa dalilin sauya ra’ayin Najeriya ’Yan lokuta da aka samu hannun mutanen kasar Isra’ila a wannan lamari da duniya ta sani su ne; na daya fasa-kwaurin kudin Najeriya dalolin Amurka zuwa kasar Afirka ta Kudu da kuma faduwar jirage masu saukar ungulu a Adamawa, sai kuma kama makama da dalolin Amurka da sauransu da ba za a iya bayyana su a matsayin kare muhimman bukatun Najeriya ba. Akwai bukatar gwamnati ta yi bayanin wannan mataki da ta dauka wanda ya nuna an dauke shi ne duk da akwai yadda manufofin harkokin kasashen waje da take da su.