Yayin da aka kammala gasar wasanni ta Olympics ta bana a Tokyo, babban birnin kasar Japan, tawagar Najeriya ta kammala gasar a mataki na 74 a duniya.
Sai dai kasar ita ce zama ta takwas a kasashen da suka fafata daga nahiyar Afirka guda 54.
- Za a dawo da sufurin jiragen kasa daga Legas zuwa Kano a watan Agusta
- ADP ta yi watsi da kiran IBB na kafa jam’iyyu 2 a Najeriya
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya rawaito cewa tawagar ta Najeriya ta lashe kyaututtuka biyu, wadanda suka hada da na silba daya da kuma azufa daya bayan ’yan wasanta 55 sun wakilceta a gasar.
Yayin da Ese Brume ta lashe kyautar azurfa bayan ta zo ta uku a bangaren tsalle na mata, ita kuwa Blessing Oborududu ta lashe silba ne a bangaren kokawa na mata.
An dai fara gasar ne ranar 23 ga watan Yulin 2021 sannan aka kammala ta ranar Lahadi, inda mutum 93 daga cikin 206 da suka fafata suka ci kyaututtuka, ciki har da mutum 13 daga nahiyar Afirka.
Tuni da tawagar ’yan wasan Najeriya suka sauka a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ranar Asabar.
Sai dai kasar ta fuskanci matsaloli tun daga farkon gasar inda aka hana ’yan wasanta guda 10 fafatawa a ciki, lamarin da har sai da ya kai su ga yin zanga-zangar nuna rashin jin dadi.