✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta haye gasar cin kofin Afirka na ’yan gida

A ranar Asabar da ta wuce ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles masu yin kwallo a gida suka haye gasar cin kofin Afirka ta…

A ranar Asabar da ta wuce ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles masu yin kwallo a gida suka haye gasar cin kofin Afirka ta ’yan gida da aka fi sani da CHAN bayan kungiyar ta lallasa takwararta ta Jamhuriyyar Benin da ci 2-0.

A wasa na farko da aka yi a Jamhuriyar Benin, Super Eagles ce ta sha kashi da ci 1-0 amma a wasa na biyu da aka yi a filin wasa na Sani Abacha da ke Kano, Super Eagles ce ta lallasa Jamhuriyar Benin da ci 2-0 da hakan ya nuna kungiyar ta samu nasara ne da ci 2-1 idan aka hada sakamakon wasannin biyu.

Tun a farkon rabin lokaci ne ’yan kwallon Eagles Rabi’u Ali da Kingsley Eduwo suka zura kwallaye biyu a ragar Jamhuriyyar Benin kuma haka aka tashi wasan.

Wannan shi ne karo na uku a jere da Super Eagles take halartar gasar CHAN da ake yi duk bayan shekara biyu.

kungiyar Super Eagles dai ta halarci gasar da ta gudana a Afirka ta Kudu a shekarar 2014 da wacce ta gudana a Ruwanda a shekarar 2016 ga shi za ta halarci wacce za ta gudana a badi a kasar Kenya idan Allah Ya kaimu.