✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta haramta sayar da tikitin jirgin sama da Dala

Za a sanya takunkumi ga kamfanonin jiragen sama da ke kin sayar da tikitinsu a kudin Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta umarci Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) da ta sanya takunkumi ga kamfanonin jiragen sama na kasa da kasa da ke kin sayar da tikitinsu a kudin Naira.

Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ne ya sanar da haka bayan taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Ya ce, bayanan sirri sun nuna cewa, wasu daga kamfanonin jiragen na kin amincewa da Naira da kuma biyan kudin tikitinsu da kudin Dalar Amurka  wanda ya saba wa dokokin kasar.

Hadi Sirika, ya ce an bai wa Hukumar NCAA ta damar tunkarar duk wani kamfanin jiragen sama da ya karya doka da gangan.

Sannan ya ce, wasu daga cikin kamfanonin jiragen suna hana hukumomin tafiye-tafiye na cikin gida ta hanyar biyan kudi ta shafinsu na intanet don yin mu’amala, inda suka zabi fitar da tikiti masu tsada.

Ya yi gargadin cewa babu wani mai keta doka, komai girman matsayinsa da zai tsira idan an kama shi da aikata laifin.

Sirika ya ce, kamfanonin jiragen sama na kasashen waje sun samu sama da Dala biliyan 1.1 daga Najeriya a shekarar 2016 lokacin da Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta biya Dala miliyan 600 da ta gada daga gwamnatin da ta shude.

A cewarsa, da an ci gaba da rike kudaden shi a kasar ta hanyar kamfanin jiragen sama na Najeriya da ta samar da ayyukan yi.

Ministan ya kara da cewa, sama da Dala miliyan 265 ne kuma aka bai wa kamfanonin jiragen sama a bana daga cikin kimanin Dala miliyan 484 da aka ba su.