✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta gurfanar da ’yan kasar waje 16 a kotu kan zargin satar mai

Ana zarginsu da hada kai wajen satar mai ba bisa ka'ida ba

Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ta gurfanar da wasu ‘yan kasashen waje su 16 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Fatakwal, babban birnin jihar Ribas kan zargin satar mai.

Wadanda lamarin ya shafa na fuskantar tuhuma kan aikata laifuffuka uku, da suka hada da hadin baki da yunkurin yin harkallar mai a kebabben wuri ga Najeriya ba tare da izinin hukuma ba.

Sai dai bayan karanto musu zarge-zargen da ake yi musu, wadanda ake zargin sun musanta aikata laifukan da ake tuhumarsu.

Bayan sauraron bayanai daga bangarorin biyu, Alkalin kotun, Mai Shari’a Turaki Muhammed, ya ba da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake tuhumar a cikin jirgin ruwansu.

Daga nan, Alkali Muhammed ya dage ci gaba da shari’ar zuwa 15 ga Nuwamba don bai wa wasu daga cikin wadanda ake zargin damar ganawa da lauyoyinsu da duba lafiyarsu idan da bukatar hakan.

Jaridar Guardian ta rawaito cewa, a ranar bakwai ga Augusta sojojin ruwan Najeriya suka kama wasu ‘yan kasashen waje su 26 a yankin Akpo na Jihar Ribas suna satar mai.