✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Harbin Lekki: Hawainiyar Amnesty International ta kiyayi ramarmu – Gwamnatin Najeriya

Gwamnatin Tarayya ta gargadi kungiyar kare hakki dan-Adam ta Amnesty International kan yin katsa-landan.

Gwamnatin Tarayya ta gargadi kungiyar kare hakki dan-Adam ta Amnesty International kan yin katsa-landan kan abubuwan da ba su tabbatar ba.

Gwamnatin wacce take mayar da martani ga kungiyar kan rahotonta a zargin harbin masu zanga-zangar #EndSARS a Legas ta ce akwai dimbin kura-kurai a rahoton.

Hadimin Shugaban Kasa Muhamamdu Buhari kan Watsa Labarai, Femi Adesina ne ya bayyana haka a tattaunawarsa da gidan Talabijin na Channels a ranar Alhamis.

Ya ce, “An kona ofishin ’yan sanda na Orile. Abubuwa da dama sun faru kafin faruwar rikicin Lekki, kuma hakan ba zai zama wata hanya da za a dinga sace-sace ba.

“Amnesty International ba ta kyauta ba, domin ba kowanne rahoto take da shi ba kuma ba ita ce ke mulkin kasar nan ba. Ya kamata a ce ta fadada bincikenta.

“Ya kamata ta yi aikinta ta hanyar yin binciken da ya dace dangane da abubuwan da ’yan Najeriya suka sanar da ita,” cewar Adesina.

Ya kuma ja hankalin al’ummar Najeriya da su yi watsi da wasu rahotannin da aka yada kan hakikanin abinda ya faru tsakanin sojoji da masu zanga-zangar #EndSARS a Lekki.