Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce Najeriya ce kasar da a fi yawan yara masu dauke da cuta mai karya garkuwar jiki da tarin fuka.
Wakilin WHO a Najeriya, Dokta Walter Kazadi Mulombo ne ya bayyana haka a taron shekara-shekara karo na 6 da kungiyar ’yan jarida bangaren lafiya ta Najeriya (ANHEJ) ta shirya da hadin gwiwar WHO a Jihar Nasarawa.
Ya ce baya ga haka, Najeria ce ke da kashi 50 cikin 100 na marasa lafiyar da ba sa samun isasshiyar kulawa, a kasashe masu yanayin zafi a Afirka.
Wakilin Shugaban Kungiyar, Ahmed Khedr, ya ce duk da cewa cutar zazzabin cizon sauro ta ragu daga kashi 42 zuwa 23, kasar na ci gaba da samun gwagwgwaban kaso a yaduwar cututtuka a duniya da kashi 27, da kuma kashi 24 na mace-mace.
“A bangaren yawan mutuwar masu cututtukan da ba sa yaduwa kuma, ita ke da kashi 29, tare da kashi 29 na masu cututuukan hawan jini da ciwon suga da daji da Tamowa, da kuma kashi 22 da ke mutuwa a dan kankanin lokaci,”in ji shi.
Haka zalika ya ce bayanai na nuna duka cututtukan da mace-macen an fi samun su a cikin talakawa, basoda rashin kudin magani, da kuma zuwa asibitocin marasa inganci.