✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta fara neman kai da danyen manta a kasuwar duniya

Hakan na faruwa ne sakamakon rashin tabbas a kasuwar duniya

Ga dukkan alamu har yanzu Najeriya na ta fadi-tashin ganin ta sami wadanda za su sayi danyen man da take hakowa a daidai lokacin da yajin aiki ya tsayar da komai cak a matatun man Faransa da sauran kasashen Turai.

Bayanai dai sun nuna ko a makon da ya gabata, kadan daga man da kasar ke hakowa ta iya sayarwa, yayin da sama da jiragen ruwa 20 ke neman masaya, kamar yadda ’yan kasuwa masu kwarewa a harkar man a Afrika ta Yamma suka tabbatar.

A cewar jaridar Bloomberg, lamarin kusan iri daya ne a cikin kwana 10 da suka gabata, inda akalla jirage 20 zuwa 25, kowannensu makare da ganga miliyan daya na man, ke jibge a kasuwar.

Kasashe masu arzikin mai dai na da zabin ko dai su karya farashin su sayar da shi da rangwame, ko kuma su ci gaba da jira har zuwa lokacin da matatun man za su janye yajin aikin nasu.

Idan za a iya tunawa, Kamfanin Mai na Najeriya (NNPCL) a kwanakin baya ya sanar da nadin Jean-Marc Cordier a matsayin shugaban sashen cinikin danyen mai na kamfanin.

Bugu da kari, ko a watannin baya sai da Kungiyar Kasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC+) ta sanar da zaftare yawan man da mambobinta ke hakowa da ganga miliyan daya a kullum da nufin magance yawan faduwar farashinsa a kasuwar duniya.