✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta dauko hanyar warware matsalolinta – Albaba  

Dan Takarar Majalisar Dokoki na APC daga Jahar Katsina a Karamar Hukumar Katsina, Alhaji Ali Abu Albaba ya bayyana dokar da Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari…

Dan Takarar Majalisar Dokoki na APC daga Jahar Katsina a Karamar Hukumar Katsina, Alhaji Ali Abu Albaba ya bayyana dokar da Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya sanyawa hannu akan takarar  matasa a kowane bangaren shugabanci a matsayin cigaban siyasar da zata kai kasar nan ga gaci.

Albaba ya bayyana haka ne a yayin da yake zantawa da Aminiya a ofishinsa dake Katsina, ya ce rawar da matasa ke takawa a farfajiyar siyasa a duniya ba ma a najeriya ba, abu ne wanda a sarari yake nuni da cewa kasar nan ta gano bakin zaren warware matsalolinta, saboda muhimmancin matasa cikin kowace al’umma.

Ya ce, “Kuma zamu ce wata dama ce da ta fito a fili ta damawa da matasa ta kowace fuska a kasar nan, kuma har an fara ganin irin tasirin da matasan suke da shi a siyasance anan gida Najeriya sabanin lokacin baya da aka mayar da mu gugan yasa. Mu dauki Amurka, zamu ga irin rawar da Barack Obama ya taka a matsayinsa na matashi mai jinni a jika.”

“Haka kuma Janar Yakubu Gawon yana matashi ya shugabanci kasar, haka Shagari tun yana matashi ya fara jagoranci a lokacin Sardauna. Amma daga baya aka mayar da matasa ba komai ba, har zuwan wannan bawan Allah wanda ya yi wannan tunani na sake maido mana da martabarmu. Ko anan ma kadai zamu ce APC ta yi abin da zamu yi alfahari da shi na kawo canji a kasar nan karkashin Shugabanci Baba Buhari,” inji shi.

Haka kuma matashin ya yaba wa Gwamna Masari bisa nagartarsa da kuma adalci da hangen nesa a shugabancin Jihar Katsina, “Dauki misali da zaben fitad da gwani wanda aka yi, inda ba abin kirki wannan gwamnati ta Masari take yi wa al’umma ba, na tabbata da wakilan al’ummar ba zasu zabe shi da rinjayen kuri”u ba.”

Dan takarar ya ce, idan Allah Ya ba shi nasara ya shiga Majalisar Dokokin ta Jahar Katsina, to zai yi iya kokarinsa na ganin an ƙara inganta harkokin tsaro ta hanyar kawo kudurori gami da harkokin cigaban matasan da kaucewa bangar siyasa.