✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya na shigo da tumatirin gwangwanin Naira biliyan 11 duk shekara – Gwamnan Babban Banki

Gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana cewaNajeriya tana kashe Naira biliyan daya da miliyan dari bakwai(N1.7b) duk shekara wajen shigo da tumatirin…

Gwamnan babban bankin Najeriya Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana cewaNajeriya tana kashe Naira biliyan daya da miliyan dari bakwai(N1.7b) duk shekara wajen shigo da tumatirin gwangwani cikin kasar nan, alhali fiye da kashi 50 na tumatirin da ake nomawa a cikin gida ana asararsa ne saboda rashin ingantacciyar ma’ajiya da hanyoyin rabawa da kuma yadda kayan zai isa kasuwa.
Ya yi wannan bayanin ne a yayin da yake jawabi a wajen taron kara wa juna sani na kwana guda da aka gudanar a kan fa’idar tumatiri da hanyoyin bunkasa hada-hadarsa, da babban bankin ya shirya a otel din Transcorp Hilton a Abuja.
Gwamnan, wanda mataimakiyar gwamna mai kula da tsarin tattalin arziki Misis Sarah O.Alade ta wakilta, ya ci gaba da cewa, duk shekara Najeriya tana shigo da ton dubu 65 da 809 na tumatirin gwangwani da aka kiyasta kudinsa ya kai Naira biliyan 11 da miliyan dari bakwai.
A cewarsa, rashin ingantaccen tsarin yadda za a noma tumatiri da kuma sarrafa shi a Najeriya ya sanya ake asarar kusan kashi 50 na tumatirin da ake samarwa a kasar nan.
Y ace an shirya taron ne domin a gano hayoyin bunkasar masana’antun sarrafa tumatiri ta hanyar hadin gwiwa.
Haka kuma taron zai yi kokarin magance matsalolin da suke haifar da tarnaki ga cigaban masana’antun sarrafa tumatiri, kamar  rashin iraruwa masu kyau da rashin ingancin masana’antun tumatirin darashin muhimman kayayyakin more rayuwa da rashin muhimman bayanai da sadarwa ga wadanda abin ya shafa.
Aminiya ta gano cewa, wannan dinbin kudin da ake kashewa wajen shigo da tumatirin gwangwani zai isa a bude manyan masana’antun sarrafa tumatiri guda uku da za su samar da tumatirin gwamgwanin da ake bukata a kasar nan ba sai an shigo da shi ba, wanda hakan zai taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan.
A halin yanzu dai hamshakin attajirin nan Alhaji Aliko dangote ya yi niyyar kafa masana’antar sarrafa tumatirin gwangwani na dala miliyan 25 a Kano.
Taron kara wa juna sanin na yini guda ya samu halartar ministocin kudi da albarkatun ruwa da aikin gona da wakilan bankin manoma da wakilan gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da kuma wakilan manoma daga ka’ina a fadin kasar nan.