✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya na salwantar da sojoji masu kuruciya

Editan Aminiya, ina mika ta’aziyar mutuwar matasan sojoji, wadanda aka yi asarar rayukansu a kasar Nijar, yayin da suke tuka jirgin yaki na Alfa-jet, ranar…

Editan Aminiya, ina mika ta’aziyar mutuwar matasan sojoji, wadanda aka yi asarar rayukansu a kasar Nijar, yayin da suke tuka jirgin yaki na Alfa-jet, ranar 06/05/13). Na yi matukar bakin cikin ganin yadda matasa zaratan masu basira, ya kamata ce mu ririta su, mu tarairaye su don amfanin gaba, sai mu tura su mu kyale tsofaffin hannu.
Bayan wannan hadari na gano cewa shekarun yaran nan duk bai wuce tsakanin 26 zuwa 36. Ina tsammani Najeriya ta hjorar da su saboda su gaji magabatansu, idan girma ko tsufa ya kama su, ko kuma sun yi murabus daga aiki. Mun kashe kudi wajen horar da su, amma mun buge da salwantar da rayukansu. To nan gaba su wane ne za su gaji shugabanninsu?
Mafita ga sojojin wannan kasa, ita ce a rika hada tsohon hannu kwararre tare da yaro matashi da ke koyon aiki. Ba manufarnu mu koya  muku aikinku ba, amma ni na ga sun yi kuruciya a danka musu jirgin yaki  kirar Alfa-jet su tuka a fagen fama, ba tare da an hada su da wani babban hafsan soja ba. Allah Ya ba mu juriyar rashin Sukwaduron Lida BB.B. Ado da Flying Officer A.J. Layelmenson. Shugaban kasa da sauran wadanda hakki ya rataya akansu su dauki mataki.
Daga Hajiya Fati Abuja 07037991315

Sakonnin waya

Aminiya na debe mini kewa
Edita ka mika mini godiya ga Aminiya, abin mamaki tana debe mini kewa Daga Khadija M. Maiduguri 08135556023.

Godiya ga Abu Ibrahim
Aminiya, dan majalisar Dattawa, Alhaji Abu Ibrahim ya cika wa mutanen Matazu alkawarin da ’Yan PDP suka kasa. Don haka muna godiya gareka. Allah Ya sa ka dore da ayyukan alheri. Madatsar ruwa dai ta tabbata a garinmu, sauran al’umma su himmatu wajen aikin noman rani, don yaki da fatara da talauci. Allah Ya yi mana agaji. Amin. Daga Abubakar Lawal Na-Yahaya Giredi, Matazu 08052063065.

Mun tuba Gwamna Yuguda
Edita ka mika mana tubarmu ga Maigirma Gwamnan Jihar Bauchi, Dokta Malam Isa Yuguda, ya yafe mana laifin da muka yi masa na kin amsa kirn gwamnati, a kan abin da ta umarce mu, a taimakemu a bai wa sauran ’yan uwanmu albashinsu. Don Allah a yafe mana, a madadin malaman makaranta na karamar Hukumar Misau. Daga Malam Ahmed Buba Zadawa 07038352131.

Na daina sayen Aminiya
Aminiya ba ku da adalci. Ba na kara sayen Aminiya, tunda ba ku taba sa sakona ba. Shekaru biyu ina karanta Aminiya, na yi ta tura sako ba ku fidda man. Daga Bashir Adamu Moriki, Zamfara 07036951482.

Martanin masu aron Aminiya
Shamsu aron Aminiya ba laifinsu ba ne, laifin Aminiyar ne. Don masu sayen Aminiya sun yi mata yawa ko da ake zuwa say eta kare, har dai nan Jihar Kebbi. Don haka Edita ku kara yawan Aminiya, t ayadda za ta wadaci jama’a. Daga Ajala Motors, Birnin Kebbi, 08030534483.

Ga Hauwa Adamu Gombe
Haba malama Hauwa shibn kina cikin hayyacinki kuwa, kika yi wannan shaidar ga Goodluck? Amma bari  in tunatar da wani abu guda. Kina ina lokacin da ya dauki sama da mutum 500 ’yan Neja-Dalta ya tura su karatu kasashen waje, ba tare da ya tura na sauran sassan kasr nan ba; shin ina adalcin yake a nan? Daga Ibraheem Auwal Sanee 08032353782.

Goodluck Mazankwarai
Godiya ga Goodluck Jonathan (Mazankwarai). Edita ka dubi girman Allah ka kara ba ni dama a jaridarka mai ablabarka, Aminiya, in yi  godiya ga shugaban kasa kan Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ya gina mana a Dutsin-ma ta Jihar Katsina mai albarka tuni an fara karatu. Mun gode kwarai. Daga Amiru Isah Bakori 08075959086.

Edita ko ka daina sakon maza?
Zuwa ga Editan Aminiya na tura sako sau biyar ban gani ba, sai sakon mata kawai kake rubutawa. Ko ka daina na maza? Daga Alhaji Abdullahi Mai nama Masallacin Juma’a Jos 08035882393.

Gwamna Jang a gashuwa
Salam Edita me ya hada Gwamna Dabid Jang da labarinku na shafi na 7, mai taken “an halaka mutum 25 a fafatawar sojoji da Boko Haram a Gashuwa? Daga Gambo Sale Fagwalawa 08067421362.

Gwamna Shema ga hanyar Bakori
Assalamu alaikum. Aminiya ki mika min wannan sakon zuwa ga Gwamnan Jihar Katsina Ibrahim Shehu Shema, muna  son ya taimaka, kamar yadda ya saba taimakon Katsinawa, ya gyara mana hanyar Bakori wadda ta fara daga cikin Dutsen Reme, har cikin garin Bakori. Daga Bilkisu Mansir Ahmad Ruma 08145356772.

Mu karbi fom din Hisba
Salam. Aminiya ina kira samari da ’yan mata, mu rage girman kai mu yi sauri mu je Hisba mu karbi form. Mai girma  Kwankwaso yana auar da samari da zawarawa da ’yan mata. Allah Ya taimakeka, Ya b aka aljanna. Amin gwamna/ Daga Al’Ameen Kano 08038873414.

Ahmad Gulak ka ji tsoron Allah
Salam Aminiya, ina kiran Ahmad Gulak da ya ji tsoron Allah, domin duk Najeriya an san cewa abin da yake fada ba gaskiya ba ne. Allah Kuma zai tambayeka. Daga Adamu Mai Inji Kaugama, Tsohon Direban CBN. 08037015766.

Ga Iyayen yara
Salamun alaikum. Aminiya don Allah ki ba ni fili in yi kira ga iyayen yara, da su ja kunnen direbobin da ke kai musu yar amakaranta, da su daina gudu, kamar za su bar gari. Daga Fatima Usman Bauchi 07066271217.

A daina kiran aminai mata a waya
Salaam. Edita ya aka ji da mu? Ina rokon ’yan uwana masu karanta wannan jarida tamu mai farin jini, musamman maza don girman Allah su daina damun mata masu aiko da ra’ayoyinsu, ba fa muna aikowa ba ne a rika kiranmu a waya ba, yawancinmu muna da aure. Daga Khadija Zariya 08036879932.

Ga gwamna dankwambo
Assalamu alaikum. Muna mika gaisuwarmu ga Gwamnatin Jihar Gombe, kuma muna rokonsa don Allah muna son shan zumar mulkin farar hula. Mai girma Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo a taimaka mana da hanya a unguwarmu ta Kagarawal unguwa uku da kuma Malam Inna. Gaskiya muna shan wahala a sakamakon rashin hanya.Daga abdul Jalil Saidu Unguwar Kagarawal, Gombe. 07069057165.