✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

‘Najeriya na cikin kasashe 12 mafiya hadari ga rayuwar yara’

Yara 93,000 ne aka kashe a rikice-rikice a kasashen 12 cikin shekara 10 da suka wuce

Binciken kungiyar kare hakkin yara ta Save the Children ya gano cewa Najeriya na daga cikin kasashe 12 mafiya hatsari ga rayuwar yara a duniya.

Rahoton binciken ya ce akalla yara 93,236 ne aka kashe a rikice-rikice daban-daban a kasashen 12 cikin shekara 10.

Kasashen da rahoton ya ambato sun ne: Siriya, Somaliya, Afghanistan, Yemen, Najeriya, Jamhuriyar Dimokradiyyar Kwango, Mali, Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Iraki, Sudan ta Kudu, da kuma Sudan.

Rahoton, wanda ya mayar da hankali kan cin zarafin yaran ya gano cewa kusan yara 25 ne ake kashewa a kullum cikin shekaru goman.

Sanarwa da shugabar kungiyar, Inger Ashing ta fitar ta ce rahoton ya gano cewa a shekarar 2019, yara kusan miliyan 426 ne ke zama a yankuna da kasashe masu fama da rikice-rikice.

Hakan na nuna cewa an samu kari a kan adadin a shekarar da ta gabaceta.

Sanarwar ta kara da cewa “Baya ga wannan adadin, akwai labarai da dama na wadanda lamarin ya shafa.

“Yawancin masu aikata cin zarafin na yin watsi ne da dokokin kasa da kasa, yayin da gwamnatoci ke yin biris da lamarinsu”, inji sanarwar.