✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya na da kudin sayen kaya na wata 7 a kasa

Gwamnatin Tarayya ta ce tana da kudaden da za su ishe ta shigo da kaya daga kashen waje na tsawon wata 7. Hakan na zuwa…

Gwamnatin Tarayya ta ce tana da kudaden da za su ishe ta shigo da kaya daga kashen waje na tsawon wata 7.

Hakan na zuwa ne yayin da asusun ajiyar Najeriya na kasashen waje ya karu zuwa Dala biliyan 36, duk da tasishin bullar annobar coronavirus ga tattalin arzikin kasashe.

A hannu guda kuma, kayan da Najeriya ke samarwa a cikin gida sun karu daga kashi 1.91% zuwa 2.27%, kafin bullar annobar coronavirus wadda ta dagula tattalin arziki a fadin duniya.

Buhari ya ce a yunkurinta na farfado da tattalin arziki, Najeriya ta mayar da hankali wajen samar da wadataccen abinci da makamashi da albarkatun mai da ababen more rayuwa da sugabanci na gari.

Sai dai ya ce duk da yadda bullar COVID-19 ta dagula harkoki a fadin duniya, tsananin matsalar a Najeriya na da sauki idan aka kwatanta da tattalin arzikin wasu kashe.

Ya yi bayani cewa duk matsalar tattalar, Najeriya ta kara dala biliyan 2.58 a asusun ajiyarta ta kasashen waje wanda yanzu ya kai dala biliyan 36.